Skip to content

Ku cika sawun gaba, sannan wanda ke biye da shi, abin da aka samu tawaya daga gare shi to ya zama a cikin sawun ƙarshe ne

Daga Anas Ibnu Malik - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:

«Ku cika sawun gaba, sannan wanda ke biye da shi, abin da aka samu tawaya daga gare shi to ya zama a cikin sawun ƙarshe ne».

«أَتِمُّوا الصَّفَّ المُقَدَّمَ، ثُمَّ الَّذِي يَلِيهِ، فَمَا كَانَ مِنْ نَقْصٍ فَلْيَكُنْ فِي الصَّفِّ المُؤَخَّرِ».

Abu Dawud da Nasa'i ne suka ruwaito shi.
Ingantacce ne
Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya umarci mazaje masu yin sallah a jam'i da cika sawun farko, sannan da cika sawun da ke biye da shi, idan za’a samu wata tawaya a cikin wani sawu to wannan tawayar ta zama a sawun ƙarshe ne.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

Bayanin sunna a kan daidaita sawu.

Ya wajaba akan masallata kada su bar tawaya a cikin sawun gaba, kai tawaya ta zama a cikin sawun ƙarshe ne.

Manazarta

Sunan Abi Dawud (2/ 10) (671).

Sunanu Nasa'i (2/ 93) (818).

Kari (1)

شرح سنن أبي داود للعباد (89/ 25).