Skip to content

Shin kuna ganin cewa da ace akwai wata korama a kofar dayanku yana wanka a cikinta kowacce rana sau biyar, shin kuna zatan wani abu na dattinsa zai rage ?

Daga Abu Huraira Allah ya yarda da shi daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa:

"Shin kuna ganin cewa da ace akwai wata korama a kofar dayanku yana wanka a cikinta kowacce rana sau biyar, shin kuna zatan wani abu na dattinsa zai rage ?" Suka ce: Ba abin da zai rage dattinsa, ya ce: "To hakan tamkar salloli biyar ne, Allah Yana shafe kurakurai da su".

«أَرَأَيْتُمْ لَوْ أَنَّ نَهَرًا بِبَابِ أَحَدِكُمْ يَغْتَسِلُ فِيهِ كُلَّ يَوْمٍ خَمْسًا، مَا تَقُولُ ذَلِكَ يُبْقِي مِنْ دَرَنِهِ؟» قَالُوا: لَا يُبْقِي مِنْ دَرَنِهِ شَيْئًا، قَالَ: «فَذَلِكَ مِثْلُ الصَّلَوَاتِ الخَمْسِ، يَمْحُو اللَّهُ بِهِ الخَطَايَا».

Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Ingantacce ne
Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kamanta salloli biyar a kowanne yini da dare a kawarwa da kankarewarsu ga kananan zunubai da kurakurai da korama a kofar mutum da yake wanka a cikinta kowacce rana sau biyar, babu wani abu da zai ragu daga dattinsa.

Ma"anonin Kalmomi

...:

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

Wannan falalar ta kebanci kankare kananun zunubai ne, amma manya babu makawa daga tuba daga gare su.

Falalar yin salloli biyar da kiyayewa akansu da sharuddansu da rukunansu da wajibansu da sunnoninsu.

Manazarta

Sahih Al-Bukhari (1/ 112) (528).

Sahih Muslim (1/ 462) (667).

(1/ 282).

Kari (7)

نزهة المتقين شرح رياض الصالحين.

مجموعة من الباحثين (2/ 773).

تطريز رياض الصالحين.

لفيصل آل مبارك (ص610).

المعجم الوسيط.

النهاية في غريب الحديث والأثر.

لابن الأثير (2/ 115).