Skip to content

Shin dayanku ba ya jin tsoron idan ya dago kansa kafin liman, Allah Ya maida kansa kan jaki ko Allah Ya maida surarsa surar jaki

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:

"Shin dayanku ba ya jin tsoron idan ya dago kansa kafin liman, Allah Ya maida kansa kan jaki ko Allah Ya maida surarsa surar jaki".

«أَمَا يَخْشَى أَحَدُكُمْ - أَوْ: لاَ يَخْشَى أَحَدُكُمْ - إِذَا رَفَعَ رَأْسَهُ قَبْلَ الإِمَامِ، أَنْ يَجْعَلَ اللَّهُ رَأْسَهُ رَأْسَ حِمَارٍ، أَوْ يَجْعَلَ اللَّهُ صُورَتَهُ صُورَةَ حِمَارٍ».

Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Ingantacce ne
Bayani

Annabi - - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bayyana narko mai tsanani akan wanda ya dago kansa kafin limaminsa, Allah Ya maida kansa kan jaki, ko Ya maida surar halittarsa ta zama surar jaki.

Ma"anonin Kalmomi

...:

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

Akwai halaye hudu ga mamu tare da liman: Uku an hana, su ne: Rigayarsa da daidai da shi da jinkirta masa. Abinda ya halatta ga mamu: Bin liman.

Wajabcin mamu ya bi liman a sallah.

Narko da canja surar wanda yake dago kansa kafin liman zuwa surar jaki abu ne mai yiwuwa, shi ne shafewa.

Manazarta

Sahih Al-Bukhari (1/ 140) (691).

Sahih Muslim (1/ 321) (427).

Kari (6)

الإلمام بشرح عمدة الأحكام.

لإسماعيل الأنصاري (1/ 111).

خلاصة الكلام شرح عمدة الأحكام.

لفيصل آل مبارك (ص65).

تيسير العلام شرح عمدة الأحكام.

للبسام (ص133).