Skip to content
الحدِيد /

Aya 28

57 : 28

Aya 28 of الحدِيد (57 : 28). This page carries the verse in the Uthmani script with a translation of its meaning, at a stable URL that can be cited on its own.

الحدِيد Ayoyi 29
57 : 28

يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ ٱتَّقُواْ ٱللَّهَ وَءَامِنُواْ بِرَسُولِهِۦ يُؤۡتِكُمۡ كِفۡلَيۡنِ مِن رَّحۡمَتِهِۦ وَيَجۡعَل لَّكُمۡ نُورٗا تَمۡشُونَ بِهِۦ وَيَغۡفِرۡ لَكُمۡۚ وَٱللَّهُ غَفُورٞ رَّحِيمٞ

Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku bi Allah da taƙawa, ku yi ĩmãni da Manzon Sa Ya bã ku rabo biyu daga rahamar Sa, kuma Ya sanya muku wani haske wanda kuke yin tafiya da shi, kuma Ya gãfarta muku. Kuma Allah Mai gãfara ne, Mai rahama.

Explanation & meanings · 1
  1. Manzon Allah a nan, shi ne Muhammadu, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi. Anã umarnin ma'abũta Littãfi da su bĩ shi dõmin su sãmi rabo ninki biyu. Mãsu ĩmani a nan su ne 'Ahlul Kitãbi' na ƙwarai.