Skip to content
النِّسَاء /

Aya 5

4 : 5

Aya 5 of النِّسَاء (4 : 5). This page carries the verse in the Uthmani script with a translation of its meaning, at a stable URL that can be cited on its own.

النِّسَاء Ayoyi 176
4 : 5

وَلَا تُؤۡتُواْ ٱلسُّفَهَآءَ أَمۡوَٰلَكُمُ ٱلَّتِي جَعَلَ ٱللَّهُ لَكُمۡ قِيَٰمٗا وَٱرۡزُقُوهُمۡ فِيهَا وَٱكۡسُوهُمۡ وَقُولُواْ لَهُمۡ قَوۡلٗا مَّعۡرُوفٗا

Kada ku bai wa wãwãye dũkiyarku, wadda Allah Ya sanya ta a gare ku, kunã mãsu tsayuwa (ga gyãranta). Kuma ku ciyar da su a cikinta, kuma ku tufãtar da su, kuma ku gaya musu magana sananniya ta alhẽri.

Explanation & meanings · 1
  1. Sa'an nan yadda ake riƙon dũkiyar wãwã wanda bai san yadda ake riƙon dũkiya ba, ko dã shĩ bãligi ne, yã yi aure, kuma ko da shĩ ne yake neman dũkiyarsa da kansa; kamar da ijãra. Wannan wata hanyace ta tsaron haƙƙin mãsu rauni.