Skip to content
النِّسَاء /

Aya 35

4 : 35

Aya 35 of النِّسَاء (4 : 35). This page carries the verse in the Uthmani script with a translation of its meaning, at a stable URL that can be cited on its own.

النِّسَاء Ayoyi 176
4 : 35

وَإِنۡ خِفۡتُمۡ شِقَاقَ بَيۡنِهِمَا فَٱبۡعَثُواْ حَكَمٗا مِّنۡ أَهۡلِهِۦ وَحَكَمٗا مِّنۡ أَهۡلِهَآ إِن يُرِيدَآ إِصۡلَٰحٗا يُوَفِّقِ ٱللَّهُ بَيۡنَهُمَآۗ إِنَّ ٱللَّهَ كَانَ عَلِيمًا خَبِيرٗا

Kuma idan kun ji tsõron sãɓãwar tsakãninsu to ku aika da wani mai sulhu daga mutãnensa da wani mai sulhu daga mutãnenta. Idan sun yi nufin gyãrãwa, Allah zai daidaita tsakãninsu (ma'auran). Lalle ne Allah Yã kasance Masani Mai jarrabãwa.

Explanation & meanings · 1
  1. Hakamãni, ko masu sulhu biyu, su tafi su yi binciken abin da ya hana auren kyau, su tsawaci maras gaskiya daga cikin ma'auran, ko kuma su hukunta rabuwa da hul'i, ko ba da hul'i ba. Abin da suka hukunta alƙãlĩ ya zartar da shi.