38 : 41
وَٱذۡكُرۡ عَبۡدَنَآ أَيُّوبَ إِذۡ نَادَىٰ رَبَّهُۥٓ أَنِّي مَسَّنِيَ ٱلشَّيۡطَٰنُ بِنُصۡبٖ وَعَذَابٍ
Kuma ka ambaci bãwan Mu Ayyũba a lõkacin da ya kirãyi Ubangijinsa, ya ce: "Lalle nĩ, Shaiɗan yã shãfe ni da wahala da kuma wata azãba."
Explanation & meanings · 1
- Wannan ƙissa tanã nũna haƙuri ga riƙon iyãli, mulkin ƙasã da mulkin gida duka daidai suke, sai yadda Allah Ya yi umurni a yĩ su. Haka mallakar rai idan mutum bai bi umurnin Allah ba a cikinsu, sai su buwãye shi tsarewa, kamar yadda mulkin ƙasa ke buwãya a riƙe shi tãre da kãfirci da zãlunci.