Skip to content
Aal'Imran /

Aya 121

3 : 121

Aya 121 of Aal'Imran (3 : 121). This page carries the verse in the Uthmani script with a translation of its meaning, at a stable URL that can be cited on its own.

Aal'Imran Ayoyi 200
Sura · Aal'Imran
Hausa · Gummi
3 : 121

وَإِذۡ غَدَوۡتَ مِنۡ أَهۡلِكَ تُبَوِّئُ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ مَقَٰعِدَ لِلۡقِتَالِۗ وَٱللَّهُ سَمِيعٌ عَلِيمٌ

Kuma a lõkacin da ka yi sauko daga iyãlanka kana zaunar da mũminai a wurãren zamadõmin yãƙi, kuma Allah Mai ji ne, Masani.

Explanation & meanings · 1
  1. Misãli ne ga cewa idan kun yi ĩmãni, kuma kun yi taƙawa, to, ƙullinsu bã ya cũtar da ku da kõme, dõmin abin da ya auku a Yãƙin Uhdu ya isa misãli ga cewa, sai kun karkace daga hanya sa'an nan wani abu zai sãme ku. Asalin maganar shĩ ne, Annabi yã fita Uhdu da mutum ɗari tara da hamsin kuma kãfirai sunã dubũ uku. Annabi ya sauka a Uhdu rãnar Asabat, bakwai ga Shawwal, shekara ta uku ga Hijira, ya sanya bayansa wajen dũtsen Uhdu, ya gyãra safũfuwan mayãƙa, kuma ya zaunar da wata runduna ta maharba a gefen dũtsen da shugabancin Abdullahi ɗan Jubair. Sa'an nan ya ce musu: "Ku kãre mu da harbi, kada su zo mana daga bãya, kada ku ɗaga daga nan, mun rinjãya kõ an rinjãye mu." Sai suka sãɓãwa umurnin, don haka masĩfar Uhdu ta auku.