Skip to content
الحج /

Aya 47

22 : 47
الحج Ayoyi 78
Sura · الحج
Hausa · Gummi
22 : 47

وَيَسۡتَعۡجِلُونَكَ بِٱلۡعَذَابِ وَلَن يُخۡلِفَ ٱللَّهُ وَعۡدَهُۥۚ وَإِنَّ يَوۡمًا عِندَ رَبِّكَ كَأَلۡفِ سَنَةٖ مِّمَّا تَعُدُّونَ

Kuma sunã nẽman ka yi gaggãwa da azãba, alhãli kuwa Allah bã zai sãɓa wa'adinSa ba kuma lalle ne, yini ɗaya a wurin Ubangijinka kamar shẽkara dubu yake daga abin da kuke ƙidãyãwa.

Explanation & meanings · 1
  1. Allah bã Ya sãɓa wa'adinSa.Daɗewar rashin saukar azãba bã sãɓãwar wa'adi ba ne, ajalin azãbar ne bai zo ba.Dõmin yini guda a wurin Allah daidai yake da shekara dubu na shekarun dũniya. Sabõda haka kwana guda daidai yake da shekara dubu biyu. Sabõda haka sa'a guda ta Allahna daidai da shekara tamãnin da uku da wata huɗu.