2 : 94
قُلۡ إِن كَانَتۡ لَكُمُ ٱلدَّارُ ٱلۡأٓخِرَةُ عِندَ ٱللَّهِ خَالِصَةٗ مِّن دُونِ ٱلنَّاسِ فَتَمَنَّوُاْ ٱلۡمَوۡتَ إِن كُنتُمۡ صَٰدِقِينَ
Ka ce: "Idan Gidan Lãhira ya kasance sabõda ku ku ne kadai, a wurin Allah babu sauran mutãne, to, ku yi bũrin mutuwa, idan kun kasance mãsu gaskiya ."
Explanation & meanings · 1
- Ya shiga bãyanin ruɗuwar Yahũdu, da alfahari da iyãye, ya sanyã su har suka gina ransu, cewa sũ ne mafifitan mutãne a wurin Allah.