Skip to content
839 Hadisai

Kundin Hadisan Annabi

Tace sakamako

63 daga cikin katuna 839

Cire tacewa
"Ku yawaita tina mai rushe jin daɗi". Yana nufin mutuwa.
Hasan ne Tirmizi da Nasa'i da Ibnu Majah ne Suka Rawaito shi
Cewa shi ya kasance idan ya wayi gari yana cewa: "Ya Allah da (kiyayyewar) Ka ne muka wayi gari, kuma da (kiyayewar) Ka ne muka shiga maraice, da (al'amarin) Ka ne muka rayu, kuma da (al'amarin) Ka ne zamu mutu, kuma tashi (daga ƙabari) yana gareKa" Idan ya shiga maraice ya ce: "Da (kiyayewarka) Ka ne muka shiga maraice, kuma da (kiyayewar) Ka ne muka wayi gari, da (al'amarin) Ka zamu mutu, kuma tashi (daga ƙabari) yana gare Ka" ya ce: Wani lokaci kuma: "Makoma tana gare Ka".
Hasan ne Abu Dawud da Tirmizi da Nasa'i a cikin Alkubra da Ibnu Majah ne Suka Rawaito shi
«‌Allah Ya gafarta wa al’ummata kurakurai da mantuwa da abin da aka tilasta su akansa».
Nawawi ya ce: Hadisi ne mai kyau Ibnu Majah da Baihaki da wasun su ne suka ruwaito shi
"Ku saurara lallai cewa duniya tsinanniya ce, kuma abinda ke cikinta ma tsinanne ne, sai ambatan Allah da abinda ke jiɓintarsa da malami ko mai neman ilimi".
Hasan ne Tirmizi ne ya Rawaito shi
«Ku yi wa juna kyauta, za ku so juna».
Hasan ne Buhari a cikin Al-Adab Al-Mufrad da Abu Ya'la da Baihakisuka Rawaito shi.
«Wanda ya wayi gari daga cikinku lafiyayye a cikin jikinsa, kuma amintacce a cikin jama'arsa (ko ransa), kuma yana da abin cin yininsa, to kamar an tattaro masa duniya ne».
Hasan ne Tirmizi ne ya Rawaito shi
«Babu cuta ba cutarwa».
Hasan ne Ibnu Majah da Darakutni da wasunsu Suka ruwaito shi a matsayin Musnad.
Ba ya cikimmu wanda ya yi camfi, ko aka yi masa camfi, ko ya yi bokanci ko aka yi masa bokanci, ko ya yi tsafi ko aka yi masa tsafi. Duk wanda ya ƙulla wani ƙulli, duk wanda ya je wurin boka ya gasgata shi a kan abin da ya faɗa, to, ya kafircewa abin da aka saukar ga (Annabi) Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.
Hasan ne Bazzar ne Ya Rawaito shi