Skip to content
839 Hadisai

Kundin Hadisan Annabi

Tace sakamako

33 daga cikin katuna 839

Cire tacewa
"Ku yawaita tina mai rushe jin daɗi". Yana nufin mutuwa.
Hasan ne Tirmizi da Nasa'i da Ibnu Majah ne Suka Rawaito shi
Cewa shi ya kasance idan ya wayi gari yana cewa: "Ya Allah da (kiyayyewar) Ka ne muka wayi gari, kuma da (kiyayewar) Ka ne muka shiga maraice, da (al'amarin) Ka ne muka rayu, kuma da (al'amarin) Ka ne zamu mutu, kuma tashi (daga ƙabari) yana gareKa" Idan ya shiga maraice ya ce: "Da (kiyayewarka) Ka ne muka shiga maraice, kuma da (kiyayewar) Ka ne muka wayi gari, da (al'amarin) Ka zamu mutu, kuma tashi (daga ƙabari) yana gare Ka" ya ce: Wani lokaci kuma: "Makoma tana gare Ka".
Hasan ne Abu Dawud da Tirmizi da Nasa'i a cikin Alkubra da Ibnu Majah ne Suka Rawaito shi
"Ku saurara lallai cewa duniya tsinanniya ce, kuma abinda ke cikinta ma tsinanne ne, sai ambatan Allah da abinda ke jiɓintarsa da malami ko mai neman ilimi".
Hasan ne Tirmizi ne ya Rawaito shi
«Wanda ya wayi gari daga cikinku lafiyayye a cikin jikinsa, kuma amintacce a cikin jama'arsa (ko ransa), kuma yana da abin cin yininsa, to kamar an tattaro masa duniya ne».
Hasan ne Tirmizi ne ya Rawaito shi
"Wanda ya ci abin ci sai ya ce: Godiya ta tabbata ga Allah wanda Ya ciyar da ni wannan kuma Ya azirtani shi ba tare da wata dabara daga gareni ko ƙarfi ba, za'a gafarta masa abinda ya gabata daga zunubinsa".
Hasan ne Abu Dawud da Tirmizi da Ibnu Majah da Ahmad ne Suka Rawaito shi
Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana karantar da mu Alƙur'ani a kowanne hali muddin dai bai kasance yana da janaba ba.
Hasan ne Abu Dawud da Tirmizi da Nasa'i da Ibn Majah da Ahmad ne Suka Rawaito shi
Mafi cikar muminai a imani shi ne mafificinsu a kyawawan ɗabi’u, mafificinku shi ne mafificinku ga iyalinsa.
Hasan ne Abu Daud ne ya ruwaito shi da Kuma Tirmizi da Ahmad
«‌Falalar malami akan mai ibada kamar falalata ne akan wanda ke ƙasanku», sannan Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «‌Lallai Allah da mala'ikunSa da waɗanda ke sammai da ƙassai har tururuwa a cikin raminta kai har kifi suna addu'a ta alheri ga wanda yake koyar da mutane alheri».
Hasan ne da wani Sanadin Tirmizi ne ya ruwaito shi