Skip to content
839 Hadisai

Kundin Hadisan Annabi

Tace sakamako

25 daga cikin katuna 839

Cire tacewa
Cewa wani mutum ya zo wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ya yi masa magana a akan wani al'amari, sai ya ce: Allah Ya so kaima ka so, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Zaka daidaitani da Allah ne? Ka ce : Allah Shi kadai ya so".
Sanadinsa Hasan ne رواه ابن ماجه والنسائي في الكبرى وأحمد
Na ce: Ya Manzon Allah, menene haƙƙin matar ɗayanmu a kansa?, ya ce; "Ka ciyar da ita idan kaci, ka tufatar da ita idan ka tufatar (da kanka), ko ka yi aiki, kada ka daki fuska, kada ka munana, kuma kada ka ƙaurace sai a ɗaki".
Hasan ne Abu Dawud ne ya rawaito shi da Ibnu Majah da Ahmad.
"Ku yawaita tina mai rushe jin daɗi". Yana nufin mutuwa.
Hasan ne Tirmizi da Nasa'i da Ibnu Majah ne Suka Rawaito shi
Cewa shi ya kasance idan ya wayi gari yana cewa: "Ya Allah da (kiyayyewar) Ka ne muka wayi gari, kuma da (kiyayewar) Ka ne muka shiga maraice, da (al'amarin) Ka ne muka rayu, kuma da (al'amarin) Ka ne zamu mutu, kuma tashi (daga ƙabari) yana gareKa" Idan ya shiga maraice ya ce: "Da (kiyayewarka) Ka ne muka shiga maraice, kuma da (kiyayewar) Ka ne muka wayi gari, da (al'amarin) Ka zamu mutu, kuma tashi (daga ƙabari) yana gare Ka" ya ce: Wani lokaci kuma: "Makoma tana gare Ka".
Hasan ne Abu Dawud da Tirmizi da Nasa'i a cikin Alkubra da Ibnu Majah ne Suka Rawaito shi
«‌Allah Ya gafarta wa al’ummata kurakurai da mantuwa da abin da aka tilasta su akansa».
Nawawi ya ce: Hadisi ne mai kyau Ibnu Majah da Baihaki da wasun su ne suka ruwaito shi
"Ku saurara lallai cewa duniya tsinanniya ce, kuma abinda ke cikinta ma tsinanne ne, sai ambatan Allah da abinda ke jiɓintarsa da malami ko mai neman ilimi".
Hasan ne Tirmizi ne ya Rawaito shi
«Wanda ya wayi gari daga cikinku lafiyayye a cikin jikinsa, kuma amintacce a cikin jama'arsa (ko ransa), kuma yana da abin cin yininsa, to kamar an tattaro masa duniya ne».
Hasan ne Tirmizi ne ya Rawaito shi
«Babu cuta ba cutarwa».
Hasan ne Ibnu Majah da Darakutni da wasunsu Suka ruwaito shi a matsayin Musnad.