عربي - Arabic English Qafár af - Afar Afrikaans - Afrikanns Akan Shqip - Albanian አማርኛ - Amharic Հայերեն - Armenian অসমীয়া - Assamese Azərbaycanca - Azerbaijani Bamanankan - Bambara Bassa Bemba বাংলা - Bengali Bosanski - Bosnian Български - Bulgarian မြန်မာဘာသာ - Burmese Bisaya - Cebuano Cham Нохчий - Chechen chiCheŵa - Chewa 中文 - Chinese Адыгэбзэ - Circassian Hrvatski - Croatian Česky - Czech Dagbani Dansk - Danish فارسی دری - Dari Dendi ދިވެހި ބަސް - Dhivehi Nederlands - Dutch إستوني - Estonian Suomi - Finnish Français - French Fulfulde - Fula ქართული - Georgian Deutsch - German Ελληνικά - Greek ગુજરાતી - Gujrati Kreyòl ayisyen - Haitian Creole Hausa हिन्दी - Hindi Magyar - Hungarian Igbo Indonesia - Indonesian Italiano - Italian 日本語 - Japanese Jóola - Jola ಕನ್ನಡ - Kannada Қазақша - Kazakh ភាសាខ្មែរ - Khmer Kikuyu Ikinyarwanda - Kinyarwanda Ikirundi - Kirundi 한국어 - Korean كوردی سۆرانی - kurdish كوردي kurmancî - Kurmanji Kyrgyz ລາວ - Lao latviešu - Latvian Lingala lietuvių - Lithuanian Luganda Македонски - Macedonian Maguindanaon Malagasy - Malagasy Bahasa Melayu - Malay മലയാളം - Malayalam Mandinka मराठी - Marathi Mõõré - Moore नेपाली - Nepali أنكو - NKo Norwegian ଓଡ଼ିଆ - Odia oromoo - Oromo پښتو - Pashto فارسی - Persian Polski - Polish Portuguese ਪੰਜਾਬੀ - Punjabi Română - Romanian Русский - Russian Српски - Serbian Shona සිංහල - Sinhala Slovenščina - Slovenian Soomaaliga - Somali Soninke Sesotho - Sotho Español - Spanish Kiswahili - Swahili Svenska - Swedish Tagalog Тоҷикӣ - Tajik தமிழ் - Tamil తెలుగు - Telugu ไทย - Thai ትግረኛ - Tigrinya Türkçe - Turkish Ukrainian اردو - Urdu ئۇيغۇرچە - Uyghur Ўзбек - Uzbek Việt Nam - Vietnamese Wolof Yao Yorùbá - Yoruba Zarma زولو - Zulu
839 Hadisai
Kundin Hadisan Annabi
Rukunoni
Darajar hadisi
An ruwaito a
Nuna sauran majiyoyi
Mai ruwaya
Nuna duk masu ruwaya (46)
"Ya Allah ni ina neman tsarinKa daga rinjayar bashi, da rinjayar maƙiyi, da dariyar maƙiya".
Ingantacce ne Nasa'i ne ya ruwaito shi da Ahmad.
Na ce: Ya Manzon Allah, ka sanar dani wani abu in roƙi Allah, Allah - Mai girma da ɗaukaka -shi. Ya ce: "Ka roƙi Allah lafiya", sai na zauna wasu kwanuka sannan na zo sai na ce: Ya Manzon Allah, ka sanar dani wani abu in roƙi Allah shi. Sai ya ce dani: "Ya Abbas, ya baffan Manzon Allah, ka roƙi Allah lafiya a duniya da lahira".
Ingantacce ne ta wani bangaren Tirmizi da Ahmad sun rawaito shi
"Wanda yake da mata biyu sai ya karkata zuwa ɗayansu, zai zo ranar alƙiyama alhali ɓarin jikinsa a karkace".
Ingantacce ne Abu Dawud da Tirmizi da Nasa'i da Ibn Majah da Ahmad ne Suka Rawaito shi
"Mayafin musulmi zuwa rabin ƙwauri ne, kuma babu laifi - ko babu zunubi - a tsakanin sa da idan sawu, kuma abinda ya zama ƙasa da idan sawu to shi yana cikin wuta, wanda ya ja mayafinsa (ƙasa) dan girman kai to Allah ba zai yi duba zuwa gareshi ba".
Ingantacce ne Abu Dawud ne ya rawaito shi da Ibnu Majah da Ahmad.
"Addu'a ita ce ibada', sannan ya karanta; " {Ubangijinku Ya ce ku roƙeni zan amsa muku, lallai waɗanda suke girman kai game da bautata za su shiga Jahannama suna ƙasƙantattu} [Gafir: 60].
Ingantacce ne Abu Dawud da Tirmizi da Ibnu Majah da Ahmad ne Suka Rawaito shi
«Wanda ya nemi sanin wani ilimi daga abinda ake neman zatin Allah - Mai girma da ɗaukaka - da shi ba ya nemansa sai dan ya samu wata haja ta duniya da shi ba zai ji ƙanshin aljanna ba a ranar alƙima» wato ƙanshinta.
Ingantacce ne Abu Dawud ne ya rawaito shi da Ibnu Majah da Ahmad.
Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya koya mana jawabin fara magana:
Lalle godiya ta tabbata ga Allah, muna neman taimakonSa, muna neman gafararSa, muna neman tsari daga sharrin kawunammu, wanda Allah Ya shiryar babu mai ɓatar da shi, wanda ya ɓatar babu mai shiryar da shi. Ina shaidawa babu abin bautawa da cancanta sai Allah, ina kuma shaidawa [Annabi] Muhammad bawanSa ne, kuma ManzonSa ne. {Ya ku mutane ku ji tsoron Ubangijinku, Wanda Ya halicceku daga rai guda ɗaya, Ya halitta masa matarsa daga shi, daga su ya yaɗa maza da yawa da mata, Ku ji tsoron Allah Wanda ku ke magiya da Shi, (ku kiyaye) da zumunta, lalle Allah Ya kasance Mai kula da ku ne}.
{Ya ku waɗanda ku ka yi imani ku ji tsoron Allah haƙiƙanin jin tsoronSa, kada ku mutu face kuna Musulmai}.
{Ya ku waɗanda suka yi imani ku ji tsoron Allah, ku faɗi magana ta daidai, zai gyara muku ayyukanku, kuma Ya gafarta muku zunubanku, duk wanda Ya yi wa Allah da ManzonSa biyayya, to, haƙiƙa ya rabauta, rabauta mai girman gaske.
Ingantacce ne Abu Dawud da Tirmizi da Nasa'i da Ibn Majah da Ahmad ne Suka Rawaito shi
"Alkiyama ba zata tsaya ba har sai zamani ya kusantowa juna, sai shekara ta zama kamar wata, wata kuma ya zama kamar Juma'a (sati guda), Juma'a kuma ta zama kamar yini, yini ya zama kamar awa, awa kuma ta zama kamar konewar ganyen dabino".
Ingantacce ne Ahmad ne ya rawaito shi