Skip to content
839 Hadisai

Kundin Hadisan Annabi

Tace sakamako

39 daga cikin katuna 839

Cire tacewa
"Wanda ya gamu da Allah ba ya tarayya da shi da wani to zai shiga Aljanna, wanda kuma ya gamu da shi yana shirka da shi to zai shiga wuta".
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi
«Haƙiƙa ka yi tambaya game da wani abu mai girma, kuma cewa shi mai sauƙi ne ga wanda Allah Ya sawwaƙa masa ka bautawa Allah kada ka hada shi da kowa, ka tsaida sallah, ka bada zakka, ka azumci Ramadan, ka ziyarci Ɗakin (Allah). Sannan ya ce: Shin ba zan shiryar da kai zuwa ga ƙofofin alheri ba? Azumi garkuwa ne, sadaka tana shafe zunubi kamar yadda ruwa yake kashe wuta, da kuma sallar mutum a tsakiyar dare, sannan ya karanta: {Sasanninsu suna nisantar makwanci} har ya kai (suna aikatawa). sannan ya ce: Shin bana baka labari da asalin al'amari ba da ginshiƙinsa da kuma ƙololuwar tozansa, sai na ce: Na'am ya Manzon Allah, ya ce: Asalin al'amari shi ne Musulunci, ginshiƙinsa ita ce sallah, kuma ƙololuwar tozansa shi ne jihadi. Sannan ya ce: Shin bana baka labari ba da abinda zai haɗa haka gaba ɗaya ba? na ce: Na'am ya Manzon Allah! Sai ya riƙe harshensa kuma ya ce: Ka riƙe wannan, na ce: Ya Annabin Allah! Muma za’a kama mu da abin da muke magana da shi? sai ya ce: Babarka ta yi wabinka ! ai ba wani abu ne yake afkar da mutane ta fuskokinsu ko ta hancinsu ba sai abin da harsunansu suke girba».
Ingantacce ne Tirmizi ne ya ruwaito shi
Ba ya cikimmu wanda ya yi camfi, ko aka yi masa camfi, ko ya yi bokanci ko aka yi masa bokanci, ko ya yi tsafi ko aka yi masa tsafi. Duk wanda ya ƙulla wani ƙulli, duk wanda ya je wurin boka ya gasgata shi a kan abin da ya faɗa, to, ya kafircewa abin da aka saukar ga (Annabi) Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.
Hasan ne Bazzar ne Ya Rawaito shi
"An gina Musulunci abisa abubuwa biyar, shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma Annabi Muhammadu bawanSa ne kuma manzonSa ne, da tsaida sallah, da bada zakka, da ziyarar daki, da azimin Ramadan".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi
"An umurce ni da in yaki mutane har sai sun shaida cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah kuma (Annabi) Muhammadu Manzon Allah ne, su tsaida sallah, su bayar da zakka, idan suka aikata hakan sun tsare jinanensu da dukiyoyinsu daga gareni sai dai da hakkin Musulunci, kuma hisabinsu yana ga Allah".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Cewa shi ya cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: Shin kana ganin cewa idan na haɗu da wani mutum daga kafirai sai muka yi faɗa, sai ya daki ɗaya daga hannayena da takobi sai ya yanke shi, sannan ya fake dani da wata bishiya, sai ya ce: Na miƙa wuya ga Allah, shin zan kashe shi ya Manzon Allah bayan ya faɗeta? sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Kada ka kashe shi" sai ya ce: Ya Manzon Allah lallai cewa shi ya yanke mini ɗaya daga hannayena, sannan ya faɗi hakan bayan ya yanke mini shi? sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Kada ka kashe shi, domin cewa in ka kashe shi to shi yana matsayinka kafin ka kashe shi, kuma kai kana matsyinsa kafin ya fadi kalmarsa wacce ya fadeta".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Na ce: Ya Manzon Allah, Ibn Jud'an ya kasance a lokacin jahiliyya yana sada zumunci, yana ciyar da miskinai, shin hakan zai anfanar da shi? Sai Ya ce: "Ba zai anfanar dashi ba, Lallai shi bai taba fada ba koda yini daya: Ya Ubangiji Ka gafarta mini kuskurena ranar sakamako".
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi
"Duk mutumin da ya cewa ɗan'uwansa: Ya kai kafiri, to haƙiƙa ɗayansu ya dawo da ita (ya lazimceta), idan ya zama kamar yadda ya ce ne, inba haka bafa to zata dawo kansa".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi