Skip to content
839 Hadisai

Kundin Hadisan Annabi

Tace sakamako

2 daga cikin katuna 839

Cire tacewa
«Haƙiƙa ka yi tambaya game da wani abu mai girma, kuma cewa shi mai sauƙi ne ga wanda Allah Ya sawwaƙa masa ka bautawa Allah kada ka hada shi da kowa, ka tsaida sallah, ka bada zakka, ka azumci Ramadan, ka ziyarci Ɗakin (Allah). Sannan ya ce: Shin ba zan shiryar da kai zuwa ga ƙofofin alheri ba? Azumi garkuwa ne, sadaka tana shafe zunubi kamar yadda ruwa yake kashe wuta, da kuma sallar mutum a tsakiyar dare, sannan ya karanta: {Sasanninsu suna nisantar makwanci} har ya kai (suna aikatawa). sannan ya ce: Shin bana baka labari da asalin al'amari ba da ginshiƙinsa da kuma ƙololuwar tozansa, sai na ce: Na'am ya Manzon Allah, ya ce: Asalin al'amari shi ne Musulunci, ginshiƙinsa ita ce sallah, kuma ƙololuwar tozansa shi ne jihadi. Sannan ya ce: Shin bana baka labari ba da abinda zai haɗa haka gaba ɗaya ba? na ce: Na'am ya Manzon Allah! Sai ya riƙe harshensa kuma ya ce: Ka riƙe wannan, na ce: Ya Annabin Allah! Muma za’a kama mu da abin da muke magana da shi? sai ya ce: Babarka ta yi wabinka ! ai ba wani abu ne yake afkar da mutane ta fuskokinsu ko ta hancinsu ba sai abin da harsunansu suke girba».
Ingantacce ne Tirmizi ne ya ruwaito shi
Na kasance tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a wata tafiya, sai na wayi gari wata rana a kusa da shi alhali mu muna tafiya, sai na ce: Ya Manzon Allah ka bani labarin aikin da zai shigar dani aljanna kuma ya nisantar dani daga wuta, sai ya ce: "Haƙiƙa ka tambayeni daga wani abu mai girma, kuma shi mai sauƙi ne ga wanda Allah Ya sawwaƙa masa, ka bautawa Allah kada ka yi shirka da komai da Shi, ka tsaida sallah, ka bada zakka, ka azimci Ramadan, ka ziyarci Ɗakin Allah”, sannan ya ce: "Shin ba na shiryar dakai ba ga ƙofofin alheri: Azimi garkuwa ne, sadaka tana kashe kuskure kamar yanda ruwa yake kashe wuta, da sallar mutum a tsakiyar dare" ya ce: Sannan ya karanta: "{Sasanninsu suna nisanta daga makwantansu}, har ya kai {Suke aikatawa}". Sannan ya ce: "Shin bana baka labari da asalin al'amari gaba dayansa ba da ginshikinsa, da kololuwar tozansa?" Na ce: Eh, ya Manzon Allah, ya ce: "Asalin al'amari Musulunci, kuma ginshikinsa sallah, kuma kololuwar tozansa Jihadi" sannan ya ce: "Shin bana baka labari da abinda zai tattaro hakan gaba dayansa ba?" na ce: Eh, Ya Manzon Allah, sai ya rike harshensa ya ce: "Ka rike wannan", na ce Shin za’a kama mu da abinda muke magana da shi? ya ce: "Babarka ta yi wabinka ya Mu'az, ai ba wani abu ne yake afka mutane cikin wuta ta fuskokinsu ko ta hancinansu ba sai abinda harasansu suke girba".
Ingantacce ne a baki dayan hanyoyin sa Tirmizi da Ibnu Majah da Ahmad Suka ruwaito shi