Skip to content
839 Hadisai

Kundin Hadisan Annabi

Tace sakamako

27 daga cikin katuna 839

Cire tacewa
"Lallai tsakanin mutum da shirka da kafirci (shi ne) barin sallah".
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi
Cewa wani mutum ya tambayi Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - sai ya ce: Kana ganin idan na sallaci salloli waɗanda aka wajabta, na azimci watan Ramdan, na halatta halal, na haramta haram, ban ƙara komai akan hakan ba, zan shiga Aljanna? Ya ce : «Eh».
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi
"Wani mutum ba zai jefi wani mutum da fasiƙanci ba, kuma ba zai jefe shi da kafirci ba, sai ta dawo kansa idan m'abocinta bai zama kamar hakan ba".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
"Abubuwa guda huɗu wanda ya kasance a cikinsa to ya zama munafiki tsantsa, wanda ya kasance a tare da shi akwai wata ɗabi'a daga cikinsu to ya kasance akwai ɗabi'a ta munafunci a tare da shi har sai ya barta: Idan zai yi magana sai ya yi ƙarya, idan an ƙulla yarjejeniya da shi sai ya yi yaudara, idan ya yi alƙawari sai ya saɓa, idan an yi faɗa da shi sai ya yi fajirci".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya zantar damu alhali shi mai gaskiya ne abin gasgatawa: "Lallai cewa halittar dayanku ana tarota a cikin mahaifiyarsa yini arba'in da dare arba'in. Sannan ya zama gudan jini tamkarsa, sannan ya zama gudan tsoka tamkarsa, sannan a aiko masa da Mala'ika, a yi masa izini da kalmomi hudu, sai ya rubuta arzikinsa da ajalinsa da aikinsa, dan wuta ne ko dan Aljanna ne, sannan ya busa rai a cikinsa. Lallai dayanku zai yi aiki da aikin 'yan Aljanna har ya zama tsakaninsa da ita bai zamo ba sai zira'i, sai littafi ya rigaya agare shi sai ya yi aiki da aikin 'yan wuta sai yashiga wutar. Kuma cewa dayanku zai yi aiki da aikin 'yan wuta har ya kasance tsakaninsa da ita bai zamo ba sai zira'i, sai littafi ya rigaya akansa, sai ya aikata aikin 'yan aljanna sai ya shigeta".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Wani mutum daga mutanen Najad ya zo wurin manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - mai dattin kai, muna jin ƙarfin muryarsa, ba ma fahimtar abinda yake faɗa har ya kusanto ga manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai gashi yana tambaya game da musulunci, sai manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Salloli biyar a yini da dare" sai ya ce: Shin akwai wasu kuma akaina? ya ce: "A'a, sai dai idan ka yi nafila. Da azumin Ramadan”. Sai ya ce: Shin akwai wani kuma?. sai manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Saidai idan ka yi na nafila. Sai ya ambata masa zakka, sai ya ce: Shin akaina akwai waninta ? ya ce: "A'a, saidai idan ka yi nafila", ya ce: Sai mutumin ya juya baya, yana cewa: Na rantse da Allah, ba zan kara akan wannan ba, kuma ba zan rage daga gare su ba, sai manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce ya rabauta idan gasgata hakan".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Lallai wasu mutane daga mushrikai, sun kasance sun yi kisa sun yawaita, sun yi zina sun yawaita, sai suka zo wa (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - sai suka ce: Lallai abin da kake faɗa kuma kake kira zuwa gareshi mai kyau ne, ina ma dai ka sanar da mu cewa akwai kaffara ga abin da muka aikata, sai (faɗin Allah) ya sauka: {Waɗanda ba sa kiran wani ubangiji tare da Allah, kuma ba sa kashe rai wanda Allah Ya haramta face da haƙƙi, kuma ba sa yin zina} [Al-Furqan: 68], kuma (wannan ayar) ta sauka: {Kace: (Allah Ya ce), "Ya ku bayiNa waɗanda suka yi ɓarna a kan rayukanku! kada ku yanke ƙauna daga rahamar Allah} [Al-Zumar: 53].
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi mana sallar Asuba a Hudaibiyya a bayan (ruwan daya sauka) a wannan daren da ya wuce, lokacin da ya sallame sai ya juya ya fuskanto mutane, ya ce: "Shin kun san mai Ubangijinku Ya ce?" Suka ce: Allah da Manzonsane mafi sani, ya ce: "Mumini da kafiri sun wayi gari daga bayina" Amma wanda ya ce: An yi mana ruwa da falalar Ubangiji da rahamarSa, to wannan ya yi imani da Ni, kuma ya kafircewa taurari. Amma wanda ya ce: Da tauraro kaza da kaza, to wannan ya kafirce mi Ni kuma ya yi imani da taurari".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi