Skip to content
839 Hadisai

Kundin Hadisan Annabi

Tace sakamako

4 daga cikin katuna 839

Cire tacewa
«Allah Ya tsinewa Yahudawa da Nasara, sun riƙi ƙaburburan Annabwansu (a matsayin) masallatai» ta ce; Da badan haka ba da an bayyanar da ƙabarinsa, sai dai cewa an ji tsoron a riƙe shi a matsayin masallaci.
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Wasu mutane sun tambayi Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi dangane da bokaye, sai Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: "Su ba komai ba ne". Suka ce: Ya Ma’aikin Allah; Wani lokacin suna ba da labari sai kuma abin ya zama gaske. Sai Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce; Wannan kalmar ta gaske aljani ya fauceta ne, sai ya yi kyarkyararta a kunnen abokin harkarsa irin kyarkyarar kaza, sai su cakuɗata da ƙarya sama da ɗari.
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya shigo wurina, hakika na rufe jarkata da wani labule a jikinsa akwai hotuna, lokacin da ya gan shi sai ya yaye shi, fuskarsa ta janza ya ce : "Ya A'isha, Mafi tsananin azaba a wurin Allah a ranar Alkiyama wadanda suke kwaikwayon halittar Allah" A'isha ta ce: "Sai muka yanke shi sai muka maida shi shinfida ko shinfidu biyu".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Cewa Ummu Salama ta gayawa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cewa ta ga wata coci a kasar Habasha, ana kiranta Mariya, sai ta fadi duk abubuwan da ta gani a can na Hotuna, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wadannan wasu mutane ne idan bawa na gari ya mutu daga cikinsu, ko kuma mutumin kirki, sai su gina masallaci akan kabarinsa, kuma su yi masa wadannan hotunan, wadannan su ne ashararen mutane a wajen Allah".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi