Skip to content
839 Hadisai

Kundin Hadisan Annabi

Tace sakamako

18 daga cikin katuna 839

Cire tacewa
«Da a ce zaku dogara ga Allah haƙiƙanin dogaranSa, da Ya azirtaku kamar yadda yake azirta tsuntsu, yana wayar gari a yunwace ya kuma yi maraice cikinsa a cike».
Ingantacce ne Imam Ahmad da Tirmithi da Nasa'i da Ibnu Majah da Ibnu Hibban a cikin Sahihinsa da kuma Hakim ne Suka ruwaito shi
«Kada harshenka ya gushe yana ɗanye daga ambatan Allah».
Ingantacce ne Ahmad ne ya ruwaito shi da Tirmizi da Ibnu Majah da kuma Ibnu Hibban
"Ya ku mutane ku yaɗa sallama, ku ciyar da abinci, ku sadar da zumunci, ku yi sallah alhali mutane suna bacci, zaku shiga aljanna cikin aminci".
Ingantacce ne Tirmizi da Ibnu Majah da Ahmad Suka ruwaito shi
"Shin ba na baku labari da mafificin ayyukanku ba, kuma mafi tsarkinsu a gurin Mamallakinku, mafi ɗaukakarsu a darajojinku kuma mafi alheri agareku daga ciyar da zinari da azirfa, kuma mafi alheri agareku daga ku haɗu da maƙiyanku ku daki wuyan su, suma su daki wuyan ku?" suka ce: Eh. Ya ce: "Ambatan Allah - Maɗaukakin sarki".
Ingantacce ne Tirmizi da Ibnu Majah da Ahmad Suka ruwaito shi
"Canfi shirka ne, canfi shirka ne, canfi shirka ne, - sau uku -", babu wani a cikinmu saidai, saidai cewa Allah - Mai girma da daukaka - Yana tafiyar da shi da dogara (ga Allah).
Ingantacce ne Abu Dawud da Tirmizi da Ibnu Majah da Ahmad ne Suka Rawaito shi
Cewa su sun ce: Ya Manzon Allah, lallai mu mun kasance muna ci ba ma ƙoshi, ya ce: «Wataƙila kuna ci ne a rarrabe?» Ya ce: Eh. Ya ce: «To ku haɗu akan abincinku, kuma ku ambaci sunan Allah akansa, za'a sanya muku albarka a cikinsa».
Hasan ne Abu Dawud ne ya rawaito shi da Ibnu Majah da Ahmad.
"Kada harshenka ya gushe yana ɗanye daga ambatan Allah".
Ingantacce ne Tirmizi da Ibnu Majah da Ahmad Suka ruwaito shi
"Babu wasu musulmai biyu da zasu haɗu sannan su gaisa hannu da hannu sai an gafarta musu kafin su rabu".
Ingantacce ne a baki dayan hanyoyin sa Abu Dawud da Tirmizi da Ibnu Majah da Ahmad ne Suka Rawaito shi