Skip to content
839 Hadisai

Kundin Hadisan Annabi

Tace sakamako

6 daga cikin katuna 839

Cire tacewa
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi alwala sau ɗaiɗai.
Ingantacce ne Bukhari ne ya rawaito shi.
Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance Sa’i ɗaya na ruwa yana isarsa a wankan tsarki, kuma musun Nabiy ɗaya yana isarsa a alwala.
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana wanka, ko ya kasance yana wanka, da sa'i zuwa mudu biyar, kuma yana alwala da mudu.
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Lallai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi alwala sau biyu-biyu.
Ingantacce ne Bukhari ne ya rawaito shi.
Na kasance ɗan aiken Banul Muntafiƙi - ko a cikin jama'ar Bunul Muntafiƙi - zuwa wurin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, ya ce: Lokacin da muka zo wurin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - bamu same shi agidansa ba, sai muka samu Nana A'isha uwar muminai, ya ce: Sai ta yi umarni a bamu farfesu, sai aka dafa mana, ya ce: Kuma aka zo mana da ƙina' - ƙina: Shi ne farantin da a cikinsa akwai dabino - sannan Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya zo, sai ya ce: «‌Shin kun samu wani abu ne? ko shin an yi umarni akawo muku wani abu ne?» ya ce: Mukace: Eh, ya Manzon Allah, ya ce: Mun kasance tare da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, lokacin da mai kiwo ya kora tumakansa zuwa garke, atare da shi akwai wani 'yar akuya tana kuka, sai ya ce: «‌Kai wane me aka haifa maka?», ya ce: 'Yar akuya, ya ce: «‌To ka yanka mana babbar akuya a madadinta», Sannan ya ce: «‌Kada ka zaci» bai ce: kada ka zaci «‌Mu saboda kaine muka yankata ba, muna da tumakai ɗari, bama so su ƙaru, idan aka haifawa makiyayin 'yar akuya, sai mu yanka babbar akuya a madadinta» Ya ce: Na ce: Ya Manzon Allah, lallai ni ina da wata mata, akwai wani abu a harshenta - yana nufin bata iya magana ba - ya ce: «‌To ka saketa», ya ce: Na ce: Ya Manzon Allah, lallai sahabiya ce, kuma ina da ɗa tare da ita, ya ce: «‌To ka umarceta» Yana cewa ka yi mata wa'azi, «‌Idan akwai alheri a tare da ita zata aikata, kada ka daki matarka kamar yadda kake dukan baiwarka», sai na ce: Ya Manzon Allah ka bani labari game da alwala, ya ce: «‌Ka cika alwala, ka tsettsefe tsakanin yatsu, ka kai matuƙa a kuskurar baki sai dai idan ka kasance mai azimi ne».
Ingantacce ne Abu Dawud ya rawaito shi, da Tirmizi da Nasa'i da Ibn Majah.
"Babu wani musulmin da zai yi alwala ya kyautata alwalarsa, sannan ya tashi ya yi sallah raka'a biyu, yana mai fuskantarsu da zuciyarsa da fuskarsa, sai aljanna ta wajaba gareshi" Ya ce: Sai na ce: Ya mamakin kyan wannan, sai ga wani mai magana a gabana yana cewa: Wacce ke gabanta ta fi kyau, sai na duba sai ga Umar ya ce: Lallai ni na ganka ka zo ɗazu, ya ce: "Babu wani daga cikinku da zai yi alwala sai ya kai matuƙa - ko sai ya cika - alwalar sannan ya ce: Ina shaida cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah kuma (Annabi) Muhammadu bawanSa ne kuma ManzonSa ne sai an buɗe masa kofofin aljanna takwas zai shiga ta wacce yake so".
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi