Skip to content
839 Hadisai

Kundin Hadisan Annabi

Tace sakamako

6 daga cikin katuna 839

Cire tacewa
"Wanda zai je Juma'a a cikinku to ya yi wanka".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance Sa’i ɗaya na ruwa yana isarsa a wankan tsarki, kuma musun Nabiy ɗaya yana isarsa a alwala.
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi
Cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya haɗu da shi a wata hanya cikin hanyoyin Madina alhali shi yana da janaba, sai ya sulale ya tafi ya yi wanka, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bibiye shi, lokacin da ya zo masa sai ya ce: «‌Ina kake ya Abu Huraira?» sai ya ce: Ya Manzon Allah ka haɗu da ni alhali ni ina da janaba sai na ƙyamaci in zauna da kai har sai na yi wanka, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «‌Tsarki ya tabbata ga Allah, lallai mumini ba ya zama najasa».
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
"Wanda ya yi wanka irin wankan janaba a ranar Juma`a, sannan ya tafi, kamar ya bayar da sadakar rakuma ne, wanda ya tafi a lokaci na biyu, kamar ya bayar da sadakar saniya ne. wanda ya tafi a lokaci na uku kamar ya bayar da sadakar rago ne mai ƙaho. wanda ya tafi a lokaci na huɗu kamar ya bayar da kaza ne, wanda kuma ya tafi a lokaci na biyar kamar ya bayar da ƙwai ne. Idan liman ya fito Mala`iku za su halarto suna sauraron zikiri (Huɗuba)".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
"Wajibi ne a kan kowanne musulmi ya yi wanka a kowanne kwana bakwai, ya wanke kansa da jikinsa".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Na ajiye wa annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - ruwan wanka, sai na kare shi da tufafi, sai ya saka a hannayensa, sai ya wankesu, sannan ya zuba da damansa akan hagunsa, sai ya wanke gabansa, sai ya goga hannunsa a kasa, sai ya shafe shi, sannan ya wanke shi, sai ya kuskure baki ya shaƙi ruwa, ya wanke fuskarsa da zira'in hannunsa biyu, sannan ya zuba a kansa sai ya kwaranyo ruwan akan jikinsa, sannan sai ya gusa kadan, sai ya wanke diga-digansa, sai na ba shi tufafi bai karɓa ba, sai ya tafi alhali yana kakkaɓe hannayensa.
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi