Skip to content
839 Hadisai

Kundin Hadisan Annabi

Tace sakamako

7 daga cikin katuna 839

Cire tacewa
Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya karanta wannan ayar: {Shi ne wanda ya saukar maka da littafi daga gareshi akwai ayoyi bayyanannu su ne mafi yawan littafi da wasu masu kama da juna, amma wadanda a cikin zukatansu akwai karkata sai suke bin abinda yake kama da juna daga gareshi dan neman fitina da neman tawilinsa, kuma babu wanda yasan tawilinsa sai Allah, matabbata a cikin ilimi suna cewa mun yi imani da shi dukkansa daga gurin Ubangijinmu ne, Ba mai tinani sai ma'abota hankula} [Aal Imran: 7]. Ta ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Idan kaga wadanda suke bin masu kama da juna daga gareshi to wadannan su ne Allah Ya ambata, to ku gujesu".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
«Ɗan Adam bai cika ƙwarya mafi sharri daga ciki ba, 'yan lomomi su ishi ɗan Adam waɗanda zasu tsaida bayansa, idan ya kasance babu makawa, to ɗaya bisa uku dan abincinsa, da ɗaya bisa uku dan abin shansa, da ɗaya bisa uku dan numfashinsa».
Ingantacce ne Imam Ahmad da Tirmizi da Nasa'i da Ibnu Majah ne Suka rawaito shi
"Kada ku nemi ilimi dan ku yi wa malamai alfahari da shi, ko ku yi musu da wawaye da shi, kuma kada ku nufi bijiro da shi a zababbun majalisai, wanda ya aikata haka to wuta wuta".
Ingantacce ne Ibnu Majah ne ya ruwaito shi
"Za'a bijiro da fitintinu akan zukata kamar tabarma kara-kara, duk zuciyar da aka cakuɗata da su sai ta yi masa baƙin ɗigo, duk zuciyar data musantasu kuwa za’a yi mata farin ɗigo, har su zama akan zukata biyu (nau'i biyu), akan farar zuciya kwatankwacin fal dutse, to wannan fitinar ba zata cutar da ita ba muddin sammai da ƙasa suna nan, ɗayar kuma baƙace ƙirin kamar kifaffiyar ƙwarya, ba ta san wani aikin alheri, kuma bata inkarin wani abin ƙi, sai abinda aka cakuɗa mata na son ranta". Huzaifa ya ce: Kuma na zantar da shi, cewa lallai tsakaninka da su akwai wata kullalliyar ƙofa ta kusa a karya ta, Umar ya ce: Shin karyawa za'a yi kaicanka? Inama dai bude ta za'a yi watakila a dawo da ita, na ce: Kuma na zantar da shi wani labarin da bana galadi ba cewa wannan kofar wani mutum ne da za'a kashe ko ya mutu. Abu Khalida ya ce: Sai na ce wa Sa'ad: Ya Abu Malik, me ake nufi da Aswad Murbadun? Ya ce: Tsananin fari a cikin baki. Ya ce: Sai na ce: To me ake nufi da al-Kuzul mujakkhiya? ya ce: Wacce aka kife.
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi
Ban bar wata fitina a baya na ba mafi cutar da Maza kamar mata ba.
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
«Imanin ɗayanku ba zai cika ba har sai son zuciyarsa ya kasance mai bi ga abin da na zo da shi».
Nawawi ya ce: Hadisi ne Ingantacce Mun rawaito shi a cikin littafin Al-Hujjah da isnadi ingantacce.
"Allah Ya buga wani misali hanya ce madaidaiciya, a gefunan hanyar biyu akwai ganuwowi biyu, a cikinsu akwai budaddun kofofi, akan kofofin akwai sakakkun labulaye, a kofar hanyar akwai wani mai kira yana cewa; Yaku mutane, ku shigo hanyar gaba daya, kada ku karkace, da wani mai kiran kuma yana kira a birbishin hanyar, idan ya yi nufin ya bude wani abu daga wadancan kofofin, zai ce: Kaicanka kada ka bude shi , domin cewa kai idan ka bude shi zaka shige shi. Tafarkin shi ne Musulunci, ganuwowin biyu kuma: Su ne iyakokin Allah, budaddun kofofin kuma: Su ne abubuwan da Allah Ya haramta, wannan mai kiran kuma akan tafarkin: Shi ne littafin Allah, mai kiran kuma a birbishin tafarkin: Mai wa'azin Allah ne (Ajiyoyin Allah) a cikin zuciyar kowane musulmi".
Ingantacce ne Tirmizi da Ahmad sun rawaito shi