عربي - Arabic English Qafár af - Afar Afrikaans - Afrikanns Akan Shqip - Albanian አማርኛ - Amharic Հայերեն - Armenian অসমীয়া - Assamese Azərbaycanca - Azerbaijani Bamanankan - Bambara Bassa Bemba বাংলা - Bengali Bosanski - Bosnian Български - Bulgarian မြန်မာဘာသာ - Burmese Bisaya - Cebuano Cham Нохчий - Chechen chiCheŵa - Chewa 中文 - Chinese Адыгэбзэ - Circassian Hrvatski - Croatian Česky - Czech Dagbani Dansk - Danish فارسی دری - Dari Dendi ދިވެހި ބަސް - Dhivehi Nederlands - Dutch إستوني - Estonian Suomi - Finnish Français - French Fulfulde - Fula ქართული - Georgian Deutsch - German Ελληνικά - Greek ગુજરાતી - Gujrati Kreyòl ayisyen - Haitian Creole Hausa हिन्दी - Hindi Magyar - Hungarian Igbo Indonesia - Indonesian Italiano - Italian 日本語 - Japanese Jóola - Jola ಕನ್ನಡ - Kannada Қазақша - Kazakh ភាសាខ្មែរ - Khmer Kikuyu Ikinyarwanda - Kinyarwanda Ikirundi - Kirundi 한국어 - Korean كوردی سۆرانی - kurdish كوردي kurmancî - Kurmanji Kyrgyz ລາວ - Lao latviešu - Latvian Lingala lietuvių - Lithuanian Luganda Македонски - Macedonian Maguindanaon Malagasy - Malagasy Bahasa Melayu - Malay മലയാളം - Malayalam Mandinka मराठी - Marathi Mõõré - Moore नेपाली - Nepali أنكو - NKo Norwegian ଓଡ଼ିଆ - Odia oromoo - Oromo پښتو - Pashto فارسی - Persian Polski - Polish Portuguese ਪੰਜਾਬੀ - Punjabi Română - Romanian Русский - Russian Српски - Serbian Shona සිංහල - Sinhala Slovenščina - Slovenian Soomaaliga - Somali Soninke Sesotho - Sotho Español - Spanish Kiswahili - Swahili Svenska - Swedish Tagalog Тоҷикӣ - Tajik தமிழ் - Tamil తెలుగు - Telugu ไทย - Thai ትግረኛ - Tigrinya Türkçe - Turkish Ukrainian اردو - Urdu ئۇيغۇرچە - Uyghur Ўзбек - Uzbek Việt Nam - Vietnamese Wolof Yao Yorùbá - Yoruba Zarma زولو - Zulu
839 Hadisai
Kundin Hadisan Annabi
Rukunoni
Darajar hadisi
An ruwaito a
Nuna sauran majiyoyi
Mai ruwaya
Nuna duk masu ruwaya (59)
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, Mu’azu yana bayan shi a kan jaki, Ya ce: Ya Mu’azu Ɗan Jabal!!)). Ya ce: Amsawarka bayan Amsawarka Ya Ma’aikin Allah da taimakawa bayan taimakawa, Ya ce; Ya "Mu’azu" Ya ce: Amsawarka bayan Amsawarka Ya Ma’aikin Allah da taimakawa bayan taimakawa sau uku [ya faɗa], ya ce: Babu wani mutum da zai shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma (Annabi) Muhammad Manzon Allah ne da gaske daga zuciayarsa sai wuta ta haramta a gareshi)). Ya ce: Ya Ma’aikin Allah shin ba na ba mutane labarin nan ba domin su yi murna? Ya ce: Za su saki jiki.
Sai Mu’azu ya ba da labarin bayan rasuwar Ma’aikin Allah gudun kada ya ɓoye ilimi.
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Wasu mutane sun tambayi Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi dangane da bokaye, sai Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: "Su ba komai ba ne". Suka ce: Ya Ma’aikin Allah; Wani lokacin suna ba da labari sai kuma abin ya zama gaske. Sai Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce; Wannan kalmar ta gaske aljani ya fauceta ne, sai ya yi kyarkyararta a kunnen abokin harkarsa irin kyarkyarar kaza, sai su cakuɗata da ƙarya sama da ɗari.
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Wani mutum daga mutanen Najad ya zo wurin manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - mai dattin kai, muna jin ƙarfin muryarsa, ba ma fahimtar abinda yake faɗa har ya kusanto ga manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai gashi yana tambaya game da musulunci, sai manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Salloli biyar a yini da dare" sai ya ce: Shin akwai wasu kuma akaina? ya ce: "A'a, sai dai idan ka yi nafila. Da azumin Ramadan”. Sai ya ce: Shin akwai wani kuma?. sai manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Saidai idan ka yi na nafila. Sai ya ambata masa zakka, sai ya ce: Shin akaina akwai waninta ? ya ce: "A'a, saidai idan ka yi nafila", ya ce: Sai mutumin ya juya baya, yana cewa: Na rantse da Allah, ba zan kara akan wannan ba, kuma ba zan rage daga gare su ba, sai manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce ya rabauta idan gasgata hakan".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
"Ni ne shugaban mutane a ranar alƙiyama, shin kun san daga menene hakan? Allah Zai tara mutane na farko da na ƙarshe a bigire ɗaya, mai kira zai jiyar da su kuma gani zai ƙetare su, rana zata kusanto, sai baƙin ciki da takaici ya kai ga mutane abinda ba za su iya ɗauka ba, kuma ba za su iya jurewa ba, sai mutane su ce: Shin bakwa ganin abinda haƙiƙa ya kai muku ? shin bakwa duba wanda zai yi muku ceto zuwa ga Ubangijinku ba? sai wasu daga mutane su ce wa wasu: Ku je gurin (annabi) Adam, sai su zo wa Adam - aminci ya tabbata agare shi - sai su ce masa: Kai ne uban mutane, Allah Ya halicceka da hannunSa, kuma Ya busa maka daga ranSa, kuma Ya umarci mala'iku sai suka yi maka sujjada, ka nema mana ceto ga Ubangijinka, shin baka ganin abinda muke cikinsa, shin baka gani zuwa abinda ya kai mana? sai Adam ya ce: Lallai Ubangijina hakika Ya yi fushi a yau bai taba irin wannan fushin ba, kuma ba zai taba yin irin wannan fushin ba, kuma lallai ni hakika Ya hanani daga bishiya sai na saba maSa, kaina kaina kaina, ku tafi zuwa wanina, ku tafi zuwa (annabi) Nuhu.
Sai su zo wa (annabi) Nuhu sai su ce: kai Nuhu, lallai kai ne farkon manzanni zuwa mutanen kasa, hakika Allah Ya ambaceka bawa mai yawan godiya, shin baka ganin abinda muke cikinsa, shin baka gani zuwa abinda ya kai mana, shin baka nema mana ceto ga Ubangijinka ba? sai ya ce: Lallai Ubangijina Ya yi fushi a yau bai taba fushi irinsa ba, kuma ba zai yi fushi a bayansa ba, kuma lallai cewa ni akwai mummunar addu'ar da na yi akan mutanena, kaina kaina kaina, ku tafi zuwa wanina, ku tafi gurin (annabi) Ibrahim.
Sai su zo wa (annabi) Ibrahim sai su ce: kai Ibrahim, kai ne Annabin Allah kuma badaɗayinSa daga mutanen ƙasa, ka nema mana ceto ga Ubangijinka, shin baka ganin abinda muke cikinsa? sai ya ce musu: Lallai Ubangijina haƙiƙa Ya yi fushi a yau fushin da bai taɓa fushi irinsa ba, kuma ba zai yi fushi a bayansa ba irinsa, lallai cewa ni na yi ƙarya sau uku, kaina kaina kaina, ku tafi zuwa wanina, ku tafi zuwa ga (annabi) Musa.
Sai su zo wa (annabi) Musa sai su ce: Kai Musa kaine Manzon Allah, Allah Ya fifitaka da saƙonninSa da kuma zancenSa akan mutane, ka nema mana ceto ga Ubangijnka, shin baka ganin abinda muke cikinsa? sai ya ce: Lallai Ubangijina hakika Ya yi fushin da bai taba fushi irinsa ba, kuma ba zai yi fushi a bayansa irinsa ba, lallai ni naa kashe wani rai da ba'a yi umarni da in kasheta ba, kaina kaina kaina, ku tafi zuwa wanina, ku tafi zuwa (annabi) Isa.
Sai su zo wa (annabi) Isa sai su ce: kai Isa, kaine Manzon Allah kuma kalmarSa da ya jefata zuwa Maryam kuma rai daga gareShi, kuma ka yi wa mutane magana a cikin shinfidar goyo, ka nema mana ceto ga Ubangijinka, shin baka ganin abinda muke cikinsa? sai Isa ya ce: Lallai Ubangijina hakika Ya yi fushin da bai taba fushi irinsa ba, kuma ba zai yi fushi a bayansa irinsa ba, ba zai anbaci wani zunubi ba, kaina kaina kaina, ku tafi zuwa wanina, ku tafi zuwa (annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -".
Sai su zo wa (annabi) Muhammad sai su ce kai ne Manzon Allah kuma cika makin Annabawa, hakika Allah Ya gafarta maka abinda ya gabata daga zunubinka da abinda ya jinkirta, ka nema mana ceto zuwa ga Ubangijinka, shin baka ganin abinda muke cikinsa? sai in tafi, sai in zo ƙarƙashin al’arshi sai infaɗi ina mai sujjada ga Ubangina, sannan Allah Ya buɗe mini daga godiyarSa da kyakkyawan yabo gareShi na wani abinda bai taɓa buɗewa wani a gabani na ba, sannan a ce: Ya Muhammad ka ɗago kanka, ka yi tambaya za'a baka shi, ka nemi ceto za'a baka ceto, sai in dago kaina, sai in ce: Al'ummata ya Ubangiji, al'ummata ya Ubangiji, al'ummata ya Uabngiji, sai ace: Ya Muhammad ka shigar daga al'ummarka wadanda babu wani hisabi akansu ta kofar dama daga kofofin aljanna, kuma su suna tarayya da mutane a koma bayan haka na kofofi".
sannan ya ce: "Na rantse da wanda raina yake a hannunSa, lalai tsakanin ginshikai biyu daga ginshikan aljanna kamar tsakanin Makka ne da Hajar, ko tsakanin Makka ne da Busra".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
«Lallai Allah Ya yardar muku da abubuwa uku, kuma Yana ƙin abubuwa uku a gareku, Yana yardar muku: Ku bauta maSa, kada ku haɗa shi da wani abu a bauta, kuma ku yi riƙo da igiyar Allah gabaɗaya kada ku rarraba. Kuma yana ƙi muku: Ƙila wa ƙala, da yawan roƙo, da kuma tozartar da dukiya».
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi
Kada ku zauna a kan kaburbura, kada kuma ku yi Sallah kuna kallonsu.
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi
Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce ga mai tabo mai tabon Abdulƙais: «Lallai kai kana da ɗabi'u biyu waɗanda Allah Yake sonsu: Haƙuri da kuma dangana».
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi
"Zan bada wannan tutar ga wani mutum mai ƙaunar Allah da ManzonSa, Allah zai yi buɗi ta hannayensa" Umar ɗan Khaɗɗab ya ce: Ban so shugabanci ba sai wannan ranar, ya ce sai na yi ɗigirgire saboda ita dan kwaɗayin a kirawoni gareta, ya ce: Sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kira Aliyu bin Abi Ɗalib - Allah Ya yarda da shi -, sai ya ba shi ita, ya ce: "Ka tafi, kada ka juya, har sai Allah Ya buɗe maka." Ya ce sai Aliyu ya tafi ɗan wani taku, sannan ya tsaya bai juya ba, sai ya yi magana: Ya Manzon Allah, akan me zan yaƙi mutane? Ya ce: "Ka yaƙesu har sai sun shaida cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah kuma Annabi Muhammad manzon Allah ne, idan suka aikta hakan to hakika sun hana jinanensu da dukiyoyinsu daga gareni sai da hakkinsu kuma hisabinsu yana ga Allah".
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi