Skip to content
839 Hadisai

Kundin Hadisan Annabi

Tace sakamako

29 daga cikin katuna 839

Cire tacewa
Na tambayi Nana A'isha abinda Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yake yi a cikin gidansa? ta ce: Ya kasance yana cikin hidimar iyalansa, idan lokacin sallah ya yi sai ya fita zuwa ga sallah.
Ingantacce ne Bukhari ne ya rawaito shi.
"Duk mayafin da ya yi ƙasa da idan sawu to yana cikin wuta".
Ingantacce ne Bukhari ne ya rawaito shi.
“Duk macen da ta yi aure ba tare da izinin waliyinta ba, to aurenta ɓatacce ne - sau uku - idan ya tare da ita, to sadakin ya kasance nata ne saboda abinda ya samu na (jima'i) daga gareta, idan suka yi jayayya to sarki (shi ne) waliyyin wanda ba shi da waliyyi".
Ingantacce ne Abu Dawud da Tirmizi da Ibnu Majah da Ahmad ne Suka Rawaito shi
«Ka taimaki ɗan'uwanka azzalimi ko wanda aka zalinta». Sai wani mutum ya ce: Ya Manzon Allah, zan taimake shi idan ya kasance wanda aka zalinta ne, shin kana ganin idan ya zama azzalimi ta yaya zan taimake shi? ya ce: «Ka kare shi - ko ka hana shi - daga zalinci; domin cewa hakan taimakonsa ne».
Ingantacce ne Bukhari ne ya rawaito shi.
Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya riƙe alhariri da hagunsa, kuma zinare da damansa, sannan ya ɗaga hannayensa da su, sai ya ce: "Lallai waɗannan biyun haramun ne ga mazan al'ummata, kuma halal ne ga matansu".
Ingantacce ne Abu Dawud da Nasa'i da ibn Majah ne Suka Rawaito shi
"Lallai cewa duniya mai zakice koriya, kuma Allah Mai gadar daku ne a cikinta, sai ya duba yaya zaku yi aiki, don haka ku ji duniya kuma ku kiyayi mata, domin cewa farkon fitinar Banu Isra'ila ta kasance a mata ne".
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi
Duniya jin daɗi ce, fiyayyen jin daɗin duniya shi ne mace ta gari.
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi
"Wanda yake da mata biyu sai ya karkata zuwa ɗayansu, zai zo ranar alƙiyama alhali ɓarin jikinsa a karkace".
Ingantacce ne Abu Dawud da Tirmizi da Nasa'i da Ibn Majah da Ahmad ne Suka Rawaito shi