Skip to content
839 Hadisai

Kundin Hadisan Annabi

Tace sakamako

5 daga cikin katuna 839

Cire tacewa
Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tsinewa namijin da ya sanya kayan mace, da macen da ta sanya kayan namiji.
Ingantacce ne Nasa'i ya rawaito shi cikin Alkubra da Ibnu Majah da ma'anarsa haka kuma Ahmad suka ruwaito shi
Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya riƙe alhariri da hagunsa, kuma zinare da damansa, sannan ya ɗaga hannayensa da su, sai ya ce: "Lallai waɗannan biyun haramun ne ga mazan al'ummata, kuma halal ne ga matansu".
Ingantacce ne Abu Dawud da Nasa'i da ibn Majah ne Suka Rawaito shi
"Wanda yake da mata biyu sai ya karkata zuwa ɗayansu, zai zo ranar alƙiyama alhali ɓarin jikinsa a karkace".
Ingantacce ne Abu Dawud da Tirmizi da Nasa'i da Ibn Majah da Ahmad ne Suka Rawaito shi
Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya koya mana jawabin fara magana: Lalle godiya ta tabbata ga Allah, muna neman taimakonSa, muna neman gafararSa, muna neman tsari daga sharrin kawunammu, wanda Allah Ya shiryar babu mai ɓatar da shi, wanda ya ɓatar babu mai shiryar da shi. Ina shaidawa babu abin bautawa da cancanta sai Allah, ina kuma shaidawa [Annabi] Muhammad bawanSa ne, kuma ManzonSa ne. {Ya ku mutane ku ji tsoron Ubangijinku, Wanda Ya halicceku daga rai guda ɗaya, Ya halitta masa matarsa daga shi, daga su ya yaɗa maza da yawa da mata, Ku ji tsoron Allah Wanda ku ke magiya da Shi, (ku kiyaye) da zumunta, lalle Allah Ya kasance Mai kula da ku ne}. {Ya ku waɗanda ku ka yi imani ku ji tsoron Allah haƙiƙanin jin tsoronSa, kada ku mutu face kuna Musulmai}. {Ya ku waɗanda suka yi imani ku ji tsoron Allah, ku faɗi magana ta daidai, zai gyara muku ayyukanku, kuma Ya gafarta muku zunubanku, duk wanda Ya yi wa Allah da ManzonSa biyayya, to, haƙiƙa ya rabauta, rabauta mai girman gaske.
Ingantacce ne Abu Dawud da Tirmizi da Nasa'i da Ibn Majah da Ahmad ne Suka Rawaito shi
Na zo wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a cikin wasu mata daga matan Madina, dan mu yi masa caffa, sai muka ce: Ya manzon Allah, zamu yi maka caffa akan kada mu hada Allah da wani abu (a bauta), kada mu yi sata ba, kada mu yi zina, kada mu zo da ƙirƙirarriyar ƙarya da zamu aikata a tsakanin hannayenmu da ƙafafuwanmu, kuma kada mu saɓa maka a wani aikin alheri, ya ce: "A abinda zaku iya da abinda zaku samu ikon yi". Ta ce: Muka ce: Allah da manzonSa ne mafi tausayi garemu, zo mu yi maka caffa ya manzon Allah, sai manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Lallai ni bana gaisawa da mata, kawai maganata ga mata dari kamar maganata ce ga mace daya, ko kwatankwacin magana ga mace ɗaya".
Ingantacce ne Tirmizi da Nasa'i da Ibnu Majah ne Suka Rawaito shi