Skip to content
839 Hadisai

Kundin Hadisan Annabi

Tace sakamako

12 daga cikin katuna 839

Cire tacewa
Daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cewa Shi ya yi hani daga bakance, ya ce: "Lallai shi ba ya zuwa da alheri, kawai ana fitar da shi ne daga marowaci".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tura wani mutum akan Zakkar Banu Sulaim, ana kiransa Ibnul Lutbiyyah, lokacin da ya zo sai ya yi masa lissafi, sai ya ce: Wannan dukiyarku ce, wannan kuma kyauta ce. Sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «‌Shin me yasa ba zaka zauna a cikin gidan babanka da babarka ba, har kyautar taka ta zo maka, idan kai mai gaskiya ne». Sannan ya yi mana huɗuba, sai ya godewa Allah kuma ya yi maSa yabo, sannan ya ce: «‌Bayan haka, lallai cewa ni ina ɗorawa mutum daga cikinku wani aiki daga abinda Allah Ya jiɓinta mini, sai ya zo sai ya ce: Wannan dukiyarku ce, wannan kuma kyautar da aka bani ce, shin yanzu ba ya zauna a gidan babansa da babarsa ba har sai kyautar tasa ta zo masa !, Wallahi ɗayanku ba zai ɗauki wani abu ba, ba tare da haƙƙinsa ba sai ya haɗu da Allah yana ɗauke da shi a ranar lahira, lallai cewa na san wani daga cikinku ya gamu da Allah yana ɗauke da raƙuminsa yana kuka, ko saniya tana kuka, ko akuya yana kuka» Sannan ya ɗaga hannunsa har sai da aka ga farin hammatarsa, yana cewa: «‌Ya Allah shin na isar ?» Ganin idona da kuma jin kunnena.
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
"Jibril bai gushe ba yana yi min wasiyya da maƙoci, har sai da na yi zaton cewa shi zai sa shi ya yi gado".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
"Duk wanda ya rantse akan wata rantsuwa alhali shi yana fajiri a cikinta dan ya ci dukiyar wani mutum musulmi, to zai gamu da Allah alhali Shi yana Mai fushi akansa". ya ce: Sai Ash'As ya ce: Wallahi a kaina hakan ya kasance; ya kasance akwai wani fili tsakanina da wani mutum cikin Yahudawa, sai ya yi min musun filin, sai na kawo shi ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce dani: "Shin kana da shaidu?" Na ce: A'a. Ya ce: Sai ya cewa Bayaahudan: "Ka rantse". Ya ce: Na ce: Ya manzon Allah, to sai ya rantse ya tafi da dukiyata. Sai Allah - Maɗaukin sarki - ya ce: {Lallai ne wadanda suke musanya alkawarin Allah da rantse-rantsensu da wani farashi dan kadan}. har zuwa ƙarshen ayar,
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
"Babu wani ma'abocin zinare ko azirfa, da ba ya bada haƙƙinsu daga garesu, sai a ranar alƙiyama ya kasance za'a ƙerasu a siffar alluna na wuta, sai a ƙona shi a kansu a cikin wutar Jahannama, sai a yi wa sasanninsa da goshinsa da bayansa lalas, duk lokacin da suka ƙone sai a dawo da su, a cikin wani yinin da gawargwadansa shekara dubu hamsin ne, har sai an yi hukunci tsakanin bayi, sai yaga hanyarsa, ko dai zuwa aljanna ko kuma zuwa wuta".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
«Ku yi wa juna kyauta, za ku so juna».
Hasan ne Buhari a cikin Al-Adab Al-Mufrad da Abu Ya'la da Baihakisuka Rawaito shi.
"Azirfa da zinare riba ne, sai hannu da hannu, alkama da alkama riba ne, sai hannu da hannu, sha'ir da sha'ir riba ne, sai hannu da hannu, dabino da dabino riba ne, sai hannu da hannu".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Na zo wa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a cikin wasu mutane daga Ash'arawa ina neman ya dauki nauyinmu, sai ya ce: "Wallahi ba zan dauki nauyinku ba, bani da abinda zan dauki nauyinku" Sannan muka zauna lokacin da Allah Ya so, sai aka zo da wasu rakuma, sai ya yi mana umarni da rakuma uku, lokacin da muka tafi sai sashinmu suka ce da sashi: Allah ba Zai yi mana albarka ba, mun zowa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - muna neman ya dauki nauyinmu sai ya yi rantsuwa cewa ba zai dauki nauyinmu ba sai kuma ya dauki nauyinmu, sai Abu Musa ya ce: sai muka zo wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai muka ambata masa hakan, sai ya ce: "Ba nine na ɗauki nauyinku ba, a’a Allah ne Ya ɗauki nauyinku, Lallai ni wallahi - in Allah Ya so - bana rantsuwa, sai inga waninta mafi alheri daga gareta. sai na yi kaffarar rantsuwata, kuma nazowa wanda shi ne mafi alherin".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi