Idan ɗayanku ya shiga masallaci to ya yi wa Annabi salati kuma ya ce: Ya Allah Ka buɗe mini ƙofofin rahamarKa
Daga Abu Huraira Allah - Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce:
«Idan ɗayanku ya shiga masallaci to ya yi wa Annabi salati kuma ya ce: Ya Allah Ka buɗe mini ƙofofin rahamarKa, idan kuma zai fita to ya yi wa Annabi sallama sannan ya ce: Ya Allah Ka tsareni daga Shaiɗan abin jefewa». (Riwayar) Hakim: «Idan zai fita to ya yi wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sallama, sannan ya ce: Ya Allah Ka tsareni daga Shaiɗan abin jefewa».
«إِذَا دَخَلَ أَحَدُكُمْ المَسْجِدَ فَلْيُسَلِّمْ عَلَى النَّبِيِّ وَلْيَقُلْ: اللَّهُمَّ افْتَحْ لِي أَبْوَابَ رَحْمَتِكَ، وَإِذَا خَرَجَ فَلْيُسَلِّمْ عَلَى النَّبِيِّ وَلْيَقُلْ: اللَّهُمَّ اعْصِمْنِي مِنْ الشَّيْطَانِ الرَّجِيمِ»، وَلِلْحَاكِمِ: «وَإِذَا خَرَجَ فَلْيُسَلِّمْ عَلَى النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ وَلْيَقُلْ: اللَّهُمَّ أَجِرْنِي مِنَ الشَّيْطَانِ الرَّجِيمِ».
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya shiryar da musulmi cewa idan ya yi nufin shiga masallaci ya yi wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - salati da faɗinsa: Ya Allah Ka yi tsira Ka yi aminci ga (Annabi) Muhammad, sannan ya ce: (Ya Allah Ka buɗe mini ƙofofin rahamarKa). Idan zai fita to ya yi wa Annabi salati sai ya ce: (Ya Allah Ka tsareni daga Shaiɗan abin jefewa). A cikin riwayar Hakim: Sai ya ce: (Ya Allah Ka tsareni daga Shaiɗan abin jefewa).
An so wannan adddu'ar a yayin shiga masallaci da fita daga cikinsa.
Gamamman Zikirin ne a kowanne masallaci har Masallaci mai alfarma.
Keɓance ambatan rahama da shiga, da kuma tsari daga Shaiɗan a fita: Cewa mai shiga zai shagaltu da abin da zai kusanto da shi zuwa ga Allah da kuma aljannarSa sai ya dace da ya ambaci rahama, idan zai fita to shi zai shiga duniya da abin da ke cikinta na abubuwan shagaltarwa, sai ya dace da ya nemi kariya da kiyayewar Allah daga Shaiɗan.
Sunanu Ibn Majah (1/ 494) (773).
Kari (4)
المستدرك على الصحيحين للحاكم (1/ 325).
شرح أبي داود للعيني (2/ 374).
شرح سنن أبي داود للعباد (66/ 3).
مرشد ذوي الحجا والحاجة إلى سنن ابن ماجه والقول المكتفى على سنن المصطفى (5/ 297).
An ambata a cikin littattafai
7 Littattafai- Hisnul muslim (Garkuwar Musulmi) daga zikirorin Alƙur’ani da Sunnahحصن المسلم«Allahummaf tahli abwaba rahmatika» «Ya Allah Ka buɗe min ƙofofin rahmarKa»[41].
- Hisnul muslim (Garkuwar Musulmi) daga zikirorin Alƙur’ani da Sunnahحصن المسلمAllahumma iftah li abwaba rahmatik Ya Allah Ka buɗe mini ƙofofin rahamarKa
- Hisnul muslim (Garkuwar Musulmi) daga zikirorin Alƙur’ani da Sunnahحصن المسلم«Ya Allah Ka tsare ni daga Shaiɗan abin korewa (daga rahamar Allah)»[43].
- Hisnul muslim (Garkuwar Musulmi) daga zikirorin Alƙur’ani da Sunnahحصن المسلمAllahumma a'simni minash shaitanir rajim Ya Allah Ka tsareni daga Shaiɗan abin korewa daga (rahamar Allah)
Kari (3)
- الذكر والدعاء والعلاج بالرقي من الكتاب والسنة"إذا دخل أحدكم المسجد فليسلم على النبي - صلى الله عليه وسلم - وليقل: اللهم افتح لي أبواب رحمتك، وإذا خرج فليسلم على النبي - صلى الله عليه وسلم - وليقل اللهم اعصمني من الشيطان الرجيم" .
- تحفة الأخيار تحفة الأخيار (ببيان جملة نافعة مما ورد في الكتاب والسنة من الأدعية والأذكار)«إِذَا دَخَلَ أَحَدُكُمُ الْمَسْجِدَ، فَلْيُسَلِّمْ عَلَى النَّبِيِّ ﷺ، وَلْيَقُلْ: اللَّهُمَّ افْتَحْ لِي أَبْوَابَ رَحْمَتِكَ، وَإِذَا خَرَجَ، فَلْيُسَلِّمْ عَلَى النَّبِيِّ ﷺ، وَلْيَقُلْ: اللَّهُمَّ اعْصِمْنِي مِنَ الشَّيْطَانِ الرَّجِيم
- رسالة في الأذكار1«إِذَا دَخَلَ أَحَدُكُمُ المَسْجِدَ فَلْيُسَلِّمْ عَلَى النَّبِيِّ صلى الله عليه وسلم ثُمَّ لْيَقُلْ...». وذَكَرَه.