Skip to content

Lalle Allah Yana son bawa mai tsoronSa, wanda ya wadatu, mai ɓoye kansa

Daga Sa’ad Ɗan Abu Waƙƙas, Allah Ya yarda da shi, ya ce: Na ji Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa:

Lalle Allah Yana son bawa mai tsoronSa, wanda ya wadatu, mai ɓoye kansa.

«إِنَّ اللهَ يُحِبُّ الْعَبْدَ التَّقِيَّ الْغَنِيَّ الْخَفِيَّ».

Muslim ne ya rawaito shi
Ingantacce ne
Bayani

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya bayyana cewa Allah mabuwayi Yana son wasu daga cikin bayinsa. Daga cikinsu akwai: Mai tsoron Allah wanda yake aikata abin da aka yi umarni, yake kuma nisantar hani. Kuma yana son: Wanda ya wadatu ga barin mutane, ya yi riƙo da Allah maɗaukaki, ba ya waigawa ga wanin Allah. Kuma yana son: Mai ɓoye kansa (wanda ba ya neman suna), mai tawalu’u, mai bauta ga Ubangijinsa, wanda ya shagaltu da abin da zai amfane shi, wanda bai damu da wani ya sanshi ba, ko wani ya yabe shi ba, ko ya burge ba.

Ma"anonin Kalmomi

....:

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

Bayanin wasu siffofi masu sanyawa a samu son Allah ga bayinsa, wadanda suke su ne, Taƙ'wa da Tawalu’u da kuma yarda da abin da Allah ya raba.

Manazarta

Sahih Muslim (4/ 2277) (2965).

Kari (9)

بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين.

لسليم الهلالي (1/ 651).

كنوز رياض الصالحين.

لمجموعة من الباحثين.

نزهة المتقين شرح رياض الصالحين.

لمجموعة من الباحثين (1/ 509).

شرح رياض الصالحين.

لابن عثيمين (3/ 509).

شرح النووي على مسلم (18/ 100).