Skip to content

Wanda ya ci abin ci sai ya ce: Godiya ta tabbata ga Allah wanda Ya ciyar da ni wannan kuma Ya azirtani shi ba tare da wata dabara daga gareni ko ƙarfi ba, za'a gafarta masa abinda ya gabata daga zunubinsa

Daga Sahlu ɗan Mu'azu ɗan Anas daga babansa ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:

"Wanda ya ci abin ci sai ya ce: Godiya ta tabbata ga Allah wanda Ya ciyar da ni wannan kuma Ya azirtani shi ba tare da wata dabara daga gareni ko ƙarfi ba, za'a gafarta masa abinda ya gabata daga zunubinsa".

«مَنْ أَكَلَ طَعَامًا فَقَالَ: الحَمْدُ لِلَّهِ الَّذِي أَطْعَمَنِي هَذَا وَرَزَقَنِيهِ مِنْ غَيْرِ حَوْلٍ مِنِّي وَلاَ قُوَّةٍ، غُفِرَ لَهُ مَا تَقَدَّمَ مِنْ ذَنْبِهِ».

Abu Dawud da Tirmizi da Ibnu Majah da Ahmad ne Suka Rawaito shi
Hasan ne
Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana kwaɗaitar da wanda ya ci wani abinci da ya godewa Allah, babu wani iko gareni a samun abinci, ko a cinsa sai ga Allah - Maɗaukakin sarki - da kuma taimakonSa, Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya yi wa wanda ya faɗi hakan bushara da cewa shi ya cancanci gafarar Allah gare shi a abinda ya shuɗe daga zunubansa ƙananu.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

An so godewa Allah - Maɗaukakin sarki - a ƙarshen cin abin ci.

Bayanin girman falalar Allah - Maɗaukakin sarki - ga bayinSa, inda Ya azirtasu kuma Ya sawwaƙa musu sabubban arziƙi , kuma Ya sanya kankare munanan ayyuka a cikin hakan.

Al'amuran bayi gabaɗayansu daga Allah ne - Mai girma da ɗaukaka -, ba da dabararsu ko ƙarfinsu ba, kuma bawa abin umarta ne da aikata sabubba.

Manazarta

Sunan Tirmizi (5/ 452) (3458).

Sunan Abi Dawud (6/ 138) (4023).

Sunanu Ibn Majah (4/ 417) (3285).

Musnad Ahmad (24/ 394) (15632).

Kari (6)

نزهة المتقين شرح رياض الصالحين.

مجموعة من الباحثين (1/ 602).

بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين.

للهلالي (2/ 54).

تاج العروس من جواهر القاموس.

للزبيدي (28/ 366).