Annamimi ba zai shiga aljanna ba
Daga Huzaifa - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana cewa;
"Annamimi ba zai shiga aljanna ba".
«لَا يَدْخُلُ الْجَنَّةَ قَتَّاتٌ».
(Annabi) Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi yana ba da labarin cewa annamimi wanda yake cirato zance a tsakanin mutane da nufin ɓata tsakaninsu shi mai cancanta ne ga uƙubar cewa ba zai shiga aljanna ba.
...:
Annamimanci yana daga manyan zunubai.
Hani daga annamimanci; saboda abin da ke cikinsa na ɓatawa da cutarwa a tsakaknin ɗaiɗaiku da jama'u.
Sahih Al-Bukhari (8/ 17) (6056).
Sahih Muslim (1/ 101) (105).
Kari (8)
شرح رياض الصالحين.
لابن عثيمين (6/ 145).
فتح ذي الجلال والإكرام شرح بلوغ المرام.
لابن عثيمين (6/ 401).
توضيح الأحكام من بلوغ المرام.
للبسام (7/ 452).
منحة العلام في شرح بلوغ المرام.
لعبد الله الفوزان (10/ 273).