Wanda ya gina masallaci saboda Allah; Allah Zai gina masa kwatankwacinsa a cikin aljanna
Daga Mahmud ɗan Labid - Allah Ya yarda da shi -:
Cewa Usman ɗan Affan ya yi nufin gina masallaci sai mutane suka ƙi hakan, suka so ya bar shi a kan yadda yake, sai ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: "Wanda ya gina masallaci saboda Allah; Allah Zai gina masa kwatankwacinsa a cikin aljanna".
أَنَّ عُثْمَانَ بْنَ عَفَّانَ أَرَادَ بِنَاءَ الْمَسْجِدِ فَكَرِهَ النَّاسُ ذَلِكَ، وَأَحَبُّوا أَنْ يَدَعَهُ عَلَى هَيْئَتِهِ، فَقَالَ: سَمِعْتُ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ: «مَنْ بَنَى مَسْجِدًا لِلهِ بَنَى اللهُ لَهُ فِي الْجَنَّةِ مِثْلَهُ».
Usman Dan Affan - Allah Ya yarda da shi - ya yi nufin sake gina masallacin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - a tsari mafi kyau daga gininsa na farko, sai mutane suka ƙi hakan; saboda abin da ke cikin yin hakan na canja ginin masallacin daga yananyin gininsa a zamanin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, masallacin ya kasance an gina shi da tubali, rufinsa kuma ya kasance na azara, sai dai Usman ya yi nufin ya gina shi da duwatsu da sumunti, sai Usman - Allah Ya yarda da shi - ya ba su labarin cewa shi ya ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: Wanda ya gina masallaci don neman yardarSa - Maɗaukakin sarki, ba don riya ko jiyarwa ba, Allah zai masa sakayya da mafifici daga jinsin aikinsa, wannan sakamakon shi ne ginawar Allah gida kwatankacinsa a aljanna.
...:
Kwaɗaitarwa a kan gina masallatai da falalar hakan.
Kara girman masallaci da sabunta shi ya shiga falalar ginin.
Muhimmancin tsarkake niyya saboda Allah - Maɗaukakin sarki - a dukkanin ayyuka.
Sahih Al-Bukhari (1/ 97) (450).
Sahih Muslim (4/ 2287) (533).
Kari (4)
المفهم لما أشكل من تلخيص كتاب مسلم (2/ 131).
شرح النّووي على مسلم (5/14).
التوضيح لشرح الجامع الصحيح (5/537).
البحر المحيط الثجاج في شرح صحيح الإمام مسلم بن الحجاج (12/ 171).