Alƙiyama ba zata tashi ba har sai mutane sun dinga yin alfari da massalatai
Daga Anas - Allah Ya yarda da shi - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
«Alƙiyama ba zata tashi ba har sai mutane sun dinga yin alfari da massalatai».
«لَا تَقُومُ السَّاعَةُ حَتَّى يَتَبَاهَى النَّاسُ فِي الْمَسَاجِدِ».
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa: Yana daga cikin alamomin kusancin ranar alƙiyama da kuma ƙarewar duniya mutane zasu dinga alfahari da ƙawata masallatansu, ko kuma alfaharinsu da duniyarsu a cikin masallatan da ba'a ginasu ba sai dan ambatan Allah.
Haramcin yin alfahari da masallatai, kuma hakan aiki ne ba karɓaɓɓe ba; domin ba'a aikata shi saboda Allah ba.
Hani daga ƙawata masallatai da kaloli, da kuma fenti kala-kala da kuma zane-zane, da rubce-rubuce; dan abinda ke cikinsu na shagaltar da masallata a yayin kallonsu.
Sindi ya ce: Wannan hadisin yana daga abinda duniya ta yi masa shaida, kuma hakan yana daga cikin jumlar mu'ujizoji bayyanannu gare shi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
Sunan Abi Dawud (1/ 337) (449).
Sunanu Nasa'i (2/ 32) (689).
Sunanu Ibn Majah (1/ 475) (739).
Kari (4)
توضيح الأحكام مِن بلوغ المرام.
لعبد الله البسام (2/ 137).
فتح ذي الجلال والإكرام شرح بلوغ المرام.
لابن عثيمين (1/ 621).