Skip to content

Babu sallah in akwai abinci a gaban [mutum], ko kuma a lokacin yana matse najasa biyu, (fitsari da bayan gida)

Daga Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa:

"Babu sallah in akwai abinci a gaban [mutum], ko kuma a lokacin yana matse najasa biyu, (fitsari da bayan gida).

«لَا صَلَاةَ بِحَضْرَةِ الطَّعَامِ، وَلَا هُوَ يُدَافِعُهُ الْأَخْبَثَانِ».

Muslim ne ya rawaito shi
Ingantacce ne
Bayani

Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya hana sallah in a wurin akwai abincin da ran mai sallah yake sha'awarsa, kuma zuciyarsa take rataye da shi. Haka nan ya hana sallah tare da matse najasa biyu - su ne fitsari da bahaya -, saboda shagaltuwa da matse najasar.

Ma"anonin Kalmomi

...:

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

Ya kamata ga mai sallah ya nisantar da dukkanin abin da zai shagaltar da shi a cikin sallarsa kafin ya shiga cikin sallar.

Manazarta

Sahih Muslim (1/ 393) (560).

Kari (5)

شرح النووي على مسلم (5/ 46).

تيسير العلام شرح عمدة الأحكام.

للبسام (ص96).

تنبيه الأفهام شرح عمدة الأحكام.

لابن عثيمين (1/ 123).