Skip to content
839 Hadisai

Kundin Hadisan Annabi

Tace sakamako

3 daga cikin katuna 839

Cire tacewa

An ruwaito a

Mai ruwaya

Nuna duk masu ruwaya (215)
عمر بن الخطاب10 النعمان بن بشير8 حذيفة8 عبد الله بن عمرو بن العاص8 أبو موسى الأشعري7 أبو الدرداء6 أبو ذر6 عقبة بن عامر6 علي6 ‌أبي هريرة5 عبادة بن الصامت5 معاذ بن جبل5 ‌ابن عباس4 البراء4 أم عطية4 جرير بن عبد الله4 سهل بن سعد4 أبو بكرة3 أبو بن كعب3 أبو سعيد3 أبو قتادة3 أبو مسعود3 سعد بن أبي وقاص3 صهيب3 أبو أمامة2 أبو أمامة الباهلي2 أبو أيوب الأنصاري2 أبو بكر الصديق2 أبو هريرة قال2 أسامة بن زيد2 البراء بن عازب2 العباس بن عبد المطلب2 المقدام بن معدي كرب2 النبي صلى الله عليه وسلم قال2 النواس بن سمعان الأنصاري2 أم سلمة أم المؤمنين2 بريدة2 تميم الداري2 ثوبان2 حكيم بن حزام2 سعد2 شداد بن أوس2 ‌عائشة2 عبد الله بن بسر2 عبد الله بن مسعود قال2 عثمان2 عقبة بن عامر الجهني2 عمر2 عمران بن حصين2 معاوية2 أبان بن عثمان قال1 إبراهيم النخعي عن همام بن الحارث قال1 ‌ابن أبي أوفى1 ابن أبي مليكة1 ‌ابن عمر1 أبو الجعد الضمري1 أبو الحوراء السعدي قال1 أبو الهياج الأسدي قال1 أبو أمامة إياس بن ثعلبة الحارثي1 أبو أمامة قال1 أبو أيوب1 أبو بردة الأنصاري1 أبو بردة بن أبي موسى1 أبو برزة الأسلمي1 أبو بشير الأنصاري1 أبو حازم بن دينار1 أبو حازم قال1 أبو حمزة أنس بن مالك1 أبو حميد الساعدي1 أبو رقية تميم بن أوس الداري1 أبو زهير عمارة بن رؤيبة1 أبو سعيد الخدري قال1 أبو سعيد الخدري وأبي هريرة1 أبو سعيد الخدري وعن أبي هريرة1 أبو شريح1 أبو طلحة1 أبو عبد الرحمن عبد الله بن عمر بن الخطاب1 أبو عبد الله الجدلي قال1 أبو عبد الله النعمان بن بشير1 أبو عبد الله جابر بن عبد الله الأنصاري1 أبو عبس عبد الرحمن بن جبر1 أبو عمرو- وقيل1 أبو مالك الأشعري1 أبو مالك الحارث بن عاصم الأشعري1 أبو محمد عبد الله بن عمرو بن العاص1 أبو مرثد الغنوي1 أبو مسعود الأنصاري1 أبو مسعود عقبة بن عمرو الأنصاري البدري1 أبو نجيح العرباض بن سارية1 أبو هريرة رضي لله عنه قال1 أبو هريرة عبد الرحمن بن صخر1 أبو واقد الليثي1 أبو يعلى شداد بن أوس1 ‌أبي الزبير قال1 ‌أبي بن كعب1 ‌أبي حميد أو عن ‌أبي أسيد قال1 ‌أبي قتادة السلمي1 أبيه أبي موسى الأشعري1 أبيه قال1 أسماء بنت أبي بكر1 الأسود بن يزيد قال1 الأغر1 الحسن قال1 الحسين بن علي بن أبي طالب1 الزبير بن العوام1 العرباض بن سارية1 المغيرة1 المغيرة بن شعبة1 المقداد بن الأسود1 المقداد بن عمرو الكندي1 المقدام بن معديكرب1 النواس بن سمعان1 أم الدرداء و أبي الدرداء1 أم المؤمنين أم عبد الله عائشة1 أم حبيبة1 أم قيس بنت محصن1 أمير المؤمنين أبي حفص عمر بن الخطاب1 أميمة بنت رقيقة1 ‌أنس بن مالك1 إياس بن عبد الله بن أبي ذباب1 بريدة بن الحصيب1 جابر بن سمرة1 جبير بن مطعم1 جرير1 جندب1 جندب بن عبد الله1 جندب بن عبد الله القسري1 جويرية أم المؤمنين1 حارثة بن وهب الخزاعي1 حذيفة بن اليمان1 ‌حطان بن عبد الله الرقاشي قال1 خولة الأنصارية1 خولة بنت حكيم السلمية قالت1 رافع بن خديج1 رسول الله صلى الله عليه وسلم أنه قال1 زر بن حبيش قال1 زياد بن لبيد1 زيد بن أرقم1 زيد بن ثابت1 زيد بن خالد1 زيد بن خالد الجهني1 زينب بنت جحش1 سالم بن أبي الجعد قال1 سفيان بن عبد الله الثقفي1 سفينة1 سلمان1 سلمان الفارسي1 سلمة بن الأكوع1 سليمان بن صرد1 سمرة بن جندب1 سمرة بن جندب والمغيرة بن شعبة1 ‌سهل1 سهل بن حنيف1 سهل بن سعد الساعدي1 شريح بن هانئ قال1 صفوان بن محرز قال1 طارق بن أشيم الأشجعي1 طاوس أنه قال1 طلحة بن عبيد الله1 عائشة وعبد الله بن عباس1 عبادة1 عبد الرحمن بن أبي ليلى قال1 عبد الرحمن بن سمرة1 عبد الله بن الشخير1 عبد الله بن خبيب1 ‌عبد الله بن زيد1 عبد الله بن سلام1 عبد الله بن عمر وأبي هريرة1 ‌عبد الله بن عمرو بن العاص1 عبد الله بن مالك ابن بحينة1 عبد الله بن مغفل1 عبد الله بن يزيد الخطمي قال1 عبيد الله بن عدي بن الخيار قال1 عثمان بن أبي العاص1 عثمان بن أبي العاص الثقفي1 عثمان بن عفان1 عدي بن حاتم1 عرفجة1 عكرمة1 علي بن أبي طالب1 علي قال1 عمار بن ياسر1 عمر بن أبي سلمة1 عمرو بن سليم الأنصاري قال1 عمرو بن عامر عن ‌أنس بن مالك قال1 عياض بن حمار أخي بني مجاشع1 ‌قتادة رحمه الله قال1 قتادة قال1 قطبة بن مالك1 قيس بن عاصم1 كعب بن عجرة1 لقيط بن صبرة1 مالك بن أوس بن الحدثان أنه قال1 ‌محمود بن لبيد1 مصعب بن سعد قال1 مطر بن عكامس1 معاذة قالت1 معدان بن أبي طلحة اليعمري قال1 معقل بن يسار1 معقل بن يسار المزني1 ميمونة أم المؤمنين1 هشام بن حكيم بن حزام1 وائل الحضرمي قال1 ‌وراد كاتب المغيرة بن شعبة قال1 يحيى بن عمارة المازني قال1
"Akwai wani sarki a cikin waɗanda ke gabaninku, kuma ya kasance yana da wani matsafi, lokacin da ya girma, sai ya cewa sarkin: Haƙiƙa ni na girma, ka aiko min da wani yaron da zan koya masa tsafi, sai ya aika masa da wani yaron da zai koya masa, ya kasance akan hanyarsa idan ya shiga akwai mai ibada sai ya zauna a wurinsa ya ji zancensa, sai ya ƙayatar da shi, ya kasance idan zai zo wajen matsafin sai ya wuce ta wajen mai ibadar ya zauna a wurinsa, idan ya zo wajen matsafin sai ya dake shi, sai ya kai ƙarar hakan wajen mai ibadar, sai ya ce: Idan ka ji tsoron matsafin, to ka ce : Iyalaina ne suka tsareni, idan kuma ka ji tsoron iyalanka to ka ce: Matsafi ne ya tsareni. Yana cikin haka sai ga shi ya zo wajen wata babbar dabbar da ta tsare mutane, sai ya ce: A yau ne zan san cewa matsafi ne ya fi ko mai ibada ne ya fi ? sai ya ɗauki wani dutse, sai ya ce: Ya Allah idan al'amarin mai ibadar ne shi ne mafi soyuwa gareKa to Ka kashe wannan dabbar, har mutane su tafi, sai ya jefeta sai ya kasheta, mutane suka wuce, sai ya zo wajen mai ibadar sai ya ba shi labari, sai mai ibadar ya ce masa: Ya kai ɗana kai a yau ka fini, haƙiƙa al'amarinka ya kai abinda ka gani, lallai cewa kai za'a jarrabeka, idan an jarrabeka to kada ka nuna ni, yaron ya kasance yana warkar da makaho da kuturu, kuma yana bawa mutane maganin sauran cututtuka, sai wani ɗan majalisar sarki wanda ya makance ya ji, sai ya zo masa da kyaututtuka masu yawa, sai ya ce: Abinda ke nan saboda kaine na tarasu, idan ka warkar da ni, sai ya ce: Ni bana warkar da wani, kawai Allah ne Yake warkarwa, idan ka yi imani da Allah zan roƙi Allah sai Ya warkar da kai, sai ya yi imani da Allah sai Allah Ya warkar da shi, sai ya zo wajen sarkin, sai ya zauna a wurinsa kamar yadda ya kasance yana zama, sai sarkin ya ce da shi: Waye ya dawo maka da ganinka? Ya ce: Ubangijina, ya ce: Shin kana da wani Ubangijin wanina? ya ce: Ubangijina kuma Ubangijinka Shi ne Allah, sai ya kama shi bai gushe ba yana ta azabtar da shi har saida ya nuna yaron, sai aka zo da yaron, sai sarkin ya ce masa: Yakai ɗana, haƙiƙa tsafinka ya kai har kana iya warkar da makaho da kuturu kana yin kaza da kaza?! sai ya ce: Ni bana warkar da wani, kawai Allah ne Yake warkarwa, sai ya kama shi bai gusheba yana azabtar da shi har sai da ya nuna mai ibadar, sai aka zo da mai ibadar sai aka ce masa: Ka bar Addinika, sai ya ƙi, sai ya sa aka kawo masa zarto sai ya ɗora zartan a tsakiyar kansa, sai ya tsaga shi har saida ɓarikan jikinsa biyu suka faɗi, sannan aka zo da ɗan majalisar sarki sai aka ce da shi: Ka bar Addininka, sai ya ƙi, sai aka ɗora zarton akan tsakiyar kansa, sai ya tsaga shi da shi har sai da ɓangarorin jnikinsa biyu suka faɗi, sannan aka zo da yaron sai aka ce da shi: Ka bar Addininka, sai ya ƙi, sai ya miƙa shi wurin wasu jama'a daga mutanensa, sai ya ce: Ku tafi da shi zuwa dutsen kaza da kaza, ku hau dutsen da shi, idan kun kai ƙololuwarsa idan ya bar Addininsa to (ku kyale shi) inba haka ba fa to ku jeho shi, sai suka tafi da shi zuwa dutsen kaza da kaza sai suka hau dutsen da shi, sai ya ce: Ya Allah ka isar mini su da abinda Ka so, sai dutsen ya girgiza da su sai suka faɗo, sai ya zo yana tafiya zuwa wurin sarkin, sai sarkin ya ce da shi: Me mutanenka suka yi? sai ya ce: Allah Ya isar mini su, sai ya ƙara bada shi ga wasu daga cikin mutanensa sai ya ce: Ku tafi da shi ku ɗauke shi a cikin jirgin ruwa, kuje tsakiyar kogi da shi, idan ya bar Addininsa to inba haka ba fa to ku jefa shi, sai suka tafi da shi, sai ya ce: Ya Allah ka isar mini su da abinda Ka so, sai jirgin ruwan ya kife da su sai suka dilmiye, sai ya zo yana tafiya wurin sarkin, sai sarkin ya ce da shi: Me mutanenka suka yi? sai ya ce: Allah Ya isar mini su, sai ya cewa sarkin: Kai ba zaka iya kasheni ba har sai ka aikata abinda zan umarceka da shi, ya ce: Menene shi? ya ce: Ka tara mutane wuri ɗaya ka tsireni akan wani kututture, sannan ka ɗauki wani mashi daga cikin kibiyoyina, sannan ka sanya mashin a tsakiyar gwafa sannan ka ce: Da sunan Allah Ubangijin yaro, sannan ka harbeni, lallai kai idan ka aikata hakan to zaka kasheni, sai ya tara mutane a wuri ɗaya, sai ya tsire shi akan wani kututture, sannan ya ɗauki wani mashi daga cikin kibiyoyinsa sannan ya sanya mashin a cikin tsakiyar gwafa, sannan yace: Da sunan Allah Ubangijin yaro, sannan ya harbe shi sai ya faɗi ta kayakayinsa, sai ya ɗora hannunsa akan kayakayinsa sai ya mutu, sai mutane suka ce: Mun yi imani da Ubangijin yaro, sai aka zo wa sarkin sai aka ce da shi: Shin kana ganin abinda tsoro, haƙiƙa wallahi tsoronka ya faru, mutane sun yi imani, sai ya yi umarni da haƙa rami ta farkon layuka sai aka haƙa kuma aka hura wuta a cikinsu kuma ya ce: Duk wanda bai bar Addininsa ba to ku cusa shi a cikinta, ko a ce masa: Ka faɗa sai suka aikata, har sai da wata mace ta zo alhali a tare da ita akwai wani ɗanta ƙarami, sai ta tsaya taƙi kutsawa ciki, sai ɗan nata ya ce mata: Ya babata ki yi haƙuri lallai cewa ke akan gaskiya kike".
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi
’’Lamarin mumini da ban mamaki yake, dukkannin al’amuransa alheri ne, kuma hakan ba ya kasancewa ga kowa sai ga mumini ,idan abin farinciki ne ya same shi sai ya gode wa Allah sai, sai ya zamar masa alheri, idan kuma na sharri ne ya same shi sai ya yi haƙuri, shi ma sai ya zamar masa alheri’’.
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi
"Idan 'yan aljanna suka shiga aljanna, ya ce: Allah -Maɗaukakin sarki - zai ce: Kuna son wani abu ne da zan ƙaro muku shi? sai su ce: Ba Ka haskaka fusokinmu ba? kuma ba Ka shigar da mu aljannah ba, kuma Ka tseratar da mu daga wuta? ya ce: Sai a yaye hijabi, ba'a basu wani abu mafi soyuwa a gare su ba daga duba zuwa Ubanginsu - Mai girma da ɗaukaka -".
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi