Skip to content
839 Hadisai

Kundin Hadisan Annabi

Tace sakamako

85 daga cikin katuna 839

Cire tacewa
"Asiwaki mai tsarkake baki ne, mai sa yardar Ubangiji ne".
Ingantacce ne Nasa'i ne ya ruwaito shi da Ahmad.
A cikin faɗin Allah - Mai girma da ɗaukaka -: {Wanda ya nufe shi da wata fanɗara da zalinci zamu ɗanɗana masa azaba mai raɗaɗi} [al-haj: 25] ya ce: "Da a ce mutum ya yi nufin yin fanɗara alhali shi yana Adan Abyan da Allah Ya ɗanɗana masa azaba mai raɗaɗi".
Ingantacce ne Ahmad da Hakim ne suka ruwaito shi
“Duk macen da ta yi aure ba tare da izinin waliyinta ba, to aurenta ɓatacce ne - sau uku - idan ya tare da ita, to sadakin ya kasance nata ne saboda abinda ya samu na (jima'i) daga gareta, idan suka yi jayayya to sarki (shi ne) waliyyin wanda ba shi da waliyyi".
Ingantacce ne Abu Dawud da Tirmizi da Ibnu Majah da Ahmad ne Suka Rawaito shi
Na ce: Ya Manzon Allah, Ka fadamin wata magana a Musulunci da ba zan tambayi waninka game da ita ba, ya ce: "Ka ce na yi imani da Allah, sannan ka tabbatu akan hakan".
Ingantacce ne Muslim da Ahmad ne suka rawaito shi
"Ku yaƙi mushrikai da dukiyoyinku da rayukanku da kuma harsunanku".
Ingantacce ne Abu Dawud da Nasa'i haka Ahmad suka ruwaito shi
"Ku bibiyi tsakanin Hajji da Umarah, domin cewa su suna kore talauci da kuma zunubai kamar yadda zugazagi yake kore dattin ƙarfe, da zinariya, da azirfa, kuma kuɓutaccen Hajji ba shi da wani sakamako sai aljanna".
Ingantacce ne Tirmizi da Nasa'i da Ahmad ne Suka rawaito shi
Daga wata daga cikin matan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - Abu Amir ya ce: Nafi'u Ya ce: Ina zatan Nana Hafsa ce - Cewa an tambayeta game da karatun Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ta ce: Lallai ku ba zaku iya ba, ya ce: Sai aka ce mata bamu labarin yadda karatun yake. Ya ce: Sai ta yi karatun da ta yi a sake, Abu Amir ya ce: Nafi'u ya ce: Sai Ibnu Abi Mulaikah ya hakaito mana {Alhamdu lillahi rabbil Aalamin} [al-Fatiha: 2]. sannan ya yanyanke {Al-rahmanur Rahim} [al-Fatiha: 1] sannan ya yanyanke {Maliki yaumud din}.
Ingantacce ne Ahmad ne ya rawaito shi
"Wanda ya bar Juma'o'i uku dan wulaƙantar da su Allah zai yi yumƙi akan zuciyarsa".
Ingantacce ne Abu Dawud da Tirmizi da Nasa'i da Ibn Majah da Ahmad ne Suka Rawaito shi