Skip to content
839 Hadisai

Kundin Hadisan Annabi

Tace sakamako

12 daga cikin katuna 839

Cire tacewa
Cewa ya kasance tare da Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi a wasu tafiye- tafiyansa, ya ce: Sai Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya aika a lokacin munane suna wurin baccinsu Kada a bar wuyan wani raƙumi da wani abin wuya na tsirkiya, ko wani abin wuya dai sai an yanke shi.
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
التصنيف الشرعيتوحيد الألوهية، الشركموضوعات الحديثأهمية التوحيد، الشرك بالله وأقسامهمحاور التعريف بالإسلامبطلان الشرك وصوره
Cewa Ummu Salama ta gayawa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cewa ta ga wata coci a kasar Habasha, ana kiranta Mariya, sai ta fadi duk abubuwan da ta gani a can na Hotuna, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wadannan wasu mutane ne idan bawa na gari ya mutu daga cikinsu, ko kuma mutumin kirki, sai su gina masallaci akan kabarinsa, kuma su yi masa wadannan hotunan, wadannan su ne ashararen mutane a wajen Allah".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
التصنيف الشرعيأحكام المساجد، توحيد الألوهية، الشركموضوعات الحديثالتصوير، أهمية التوحيد، اتخاذ القبور مساجدمحاور التعريف بالإسلامبطلان الشرك وصوره
"Shin ba na ba ku labarin mafi girman zunubai ba?" sau uku, suka ce: na'am ya Manzon Allah, ya ce: "Yi wa Allah shirka, da saɓawa iyaye" sai ya zauna alhali ya kasance a kishingiɗe, sai ya ce: "Ku saurara da faɗar zur" ya ce: Bai gushe ba yana maimaitata har sai da muka ce: Ina ma dai ya yi shiru.
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
التصنيف الشرعيالأخلاق الذميمة، ذم المعاصي، الشركموضوعات الحديثعقوق الوالدين، قول الزور، الشرك بالله وأقسامهمحاور التعريف بالإسلامبطلان الشرك وصوره
"Babu ciratar cuta kuma babu camfi, fatan alkairi yana birgeni" ya ce: A ka ce : Menene fatan alkairi? sai ya ce: "Magana mai dadi".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
التصنيف الشرعيآداب الكلام والصمت، توحيد الألوهية، الشركموضوعات الحديثحفظ اللسان، أهمية التوحيد، الشرك بالله وأقسامهمحاور التعريف بالإسلامبطلان الشرك وصوره، محاسن الأخلاق