Skip to content
839 Hadisai

Kundin Hadisan Annabi

Tace sakamako

10 daga cikin katuna 839

Cire tacewa
«Abubuwa huɗu wanda ya kasance a cikinsu to ya kasance munafiki, idan akwai wata ɗabi'a daga cikinsu a tare da shi to ya kasance yana da ɗabi'ar munafunci har sai ya barta: Wanda idan zai yi zance sai ya yi ƙarya, idan ya yi alƙawari sai ya saɓa, idan aka yi rigima da shi sai ya yi fajirci, idan aka yi yarjejeniya da shi sai ya yi yaudara».
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi
"Abu biyu a cikin mutane su kafirci ne a cikinsu: Sukar nasaba, da kukan kera ga mamaci".
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi
'Misalin munafiki, kamar akuya ce mai kaikawo tsakanin turke biyu, tana kaikawo gurin wadannan wani lokaci da kuma zuwa wadancan a wani lokacin".
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi
"Lallai tsakanin mutum da shirka da kafirci (shi ne) barin sallah".
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi
"Wani mutum ba zai jefi wani mutum da fasiƙanci ba, kuma ba zai jefe shi da kafirci ba, sai ta dawo kansa idan m'abocinta bai zama kamar hakan ba".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
"Abubuwa guda huɗu wanda ya kasance a cikinsa to ya zama munafiki tsantsa, wanda ya kasance a tare da shi akwai wata ɗabi'a daga cikinsu to ya kasance akwai ɗabi'a ta munafunci a tare da shi har sai ya barta: Idan zai yi magana sai ya yi ƙarya, idan an ƙulla yarjejeniya da shi sai ya yi yaudara, idan ya yi alƙawari sai ya saɓa, idan an yi faɗa da shi sai ya yi fajirci".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi mana sallar Asuba a Hudaibiyya a bayan (ruwan daya sauka) a wannan daren da ya wuce, lokacin da ya sallame sai ya juya ya fuskanto mutane, ya ce: "Shin kun san mai Ubangijinku Ya ce?" Suka ce: Allah da Manzonsane mafi sani, ya ce: "Mumini da kafiri sun wayi gari daga bayina" Amma wanda ya ce: An yi mana ruwa da falalar Ubangiji da rahamarSa, to wannan ya yi imani da Ni, kuma ya kafircewa taurari. Amma wanda ya ce: Da tauraro kaza da kaza, to wannan ya kafirce mi Ni kuma ya yi imani da taurari".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
"Wanda ya gamu da Allah ba ya tarayya da shi da wani to zai shiga Aljanna, wanda kuma ya gamu da shi yana shirka da shi to zai shiga wuta".
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi