Skip to content
839 Hadisai

Kundin Hadisan Annabi

Tace sakamako

4 daga cikin katuna 839

Cire tacewa
"Lallai alƙawarin da ke tsakanin mu da su (shi ne) sallah, wanda ya barta, to, haƙiƙa ya kafirta".
Ingantacce ne Tirmizi da Nasa'i da Ibnu Majah da Ahmad ne Suka rawaito shi
"Canfi shirka ne, canfi shirka ne, canfi shirka ne, - sau uku -", babu wani a cikinmu saidai, saidai cewa Allah - Mai girma da daukaka - Yana tafiyar da shi da dogara (ga Allah).
Ingantacce ne Abu Dawud da Tirmizi da Ibnu Majah da Ahmad ne Suka Rawaito shi
"Dukkan wanda ya ɗosani wani yanki na ilimin taurari, to, haƙiƙa ya ɗosani wani yanki na tsafi, ya ƙara abin da ya ƙara".
Ingantacce ne Abu Dawud ne ya rawaito shi da Ibnu Majah da Ahmad.
Na kasance tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a wata tafiya, sai na wayi gari wata rana a kusa da shi alhali mu muna tafiya, sai na ce: Ya Manzon Allah ka bani labarin aikin da zai shigar dani aljanna kuma ya nisantar dani daga wuta, sai ya ce: "Haƙiƙa ka tambayeni daga wani abu mai girma, kuma shi mai sauƙi ne ga wanda Allah Ya sawwaƙa masa, ka bautawa Allah kada ka yi shirka da komai da Shi, ka tsaida sallah, ka bada zakka, ka azimci Ramadan, ka ziyarci Ɗakin Allah”, sannan ya ce: "Shin ba na shiryar dakai ba ga ƙofofin alheri: Azimi garkuwa ne, sadaka tana kashe kuskure kamar yanda ruwa yake kashe wuta, da sallar mutum a tsakiyar dare" ya ce: Sannan ya karanta: "{Sasanninsu suna nisanta daga makwantansu}, har ya kai {Suke aikatawa}". Sannan ya ce: "Shin bana baka labari da asalin al'amari gaba dayansa ba da ginshikinsa, da kololuwar tozansa?" Na ce: Eh, ya Manzon Allah, ya ce: "Asalin al'amari Musulunci, kuma ginshikinsa sallah, kuma kololuwar tozansa Jihadi" sannan ya ce: "Shin bana baka labari da abinda zai tattaro hakan gaba dayansa ba?" na ce: Eh, Ya Manzon Allah, sai ya rike harshensa ya ce: "Ka rike wannan", na ce Shin za’a kama mu da abinda muke magana da shi? ya ce: "Babarka ta yi wabinka ya Mu'az, ai ba wani abu ne yake afka mutane cikin wuta ta fuskokinsu ko ta hancinansu ba sai abinda harasansu suke girba".
Ingantacce ne a baki dayan hanyoyin sa Tirmizi da Ibnu Majah da Ahmad Suka ruwaito shi