Skip to content
839 Hadisai

Kundin Hadisan Annabi

Tace sakamako

3 daga cikin katuna 839

Cire tacewa
Filter
Pick a property to filter by
الفئة المستهدفة1
حجم المحتوى1
التخريج المتعدد2
التخريج المتعدد: متفق عليه
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya wuce wasu kaburbura biyu, sai ya ce: "Lallai su ana musu azaba, kuma ba’a yi musu azaba dan wani babban laifi ba, amma dayansu ya kasance ba ya suturta daga fitsari, amma dayan ya kasance yana tafiya da annamimanci" Sannan ya dauki wani danyan itacan dabino, sai ya raba shi biyu, sai ya kafa daya a kowanne kabari, suka ce: Ya Manzon Allah, meyasa ka aikata hakan, sai ya ce: "Watakila a saukaka musu muddin dai basu bushe ba".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
التصنيف الشرعيالأخلاق الذميمة، أهوال القبور، الاستنجاء وقضاء الحاجة، الحياة البرزخيةموضوعات الحديثالنميمة، الإيمان باليوم الآخر، عدم التنزه من البول
"Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, azaba ta tabbata ga larabawa daga sharrin da ya kusanto, a yau an buɗe katangar Yajuju da Majuju kwatankwacin hakan" sai ya kewaye ɗan yatsansa babba da wanda yake biye da shi. Zainab 'yar Jahsh ta ce : Sai na ce ya Manzon Allah: Shin zamu halaka alhali a cikinmu akwai salihai? ya ce: "Eh, idan barna ta yi yawa".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
التصنيف الشرعيالحياة البرزخية
"Idan aka tambayi musulmi a cikin ƙabari: Yana shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma (Annabi) Muhammad manzon Allah ne". to wannan shi ne faɗinSa: {Allah Yana tabbatar wa waɗanda suka yi imani da faɗa tabbatacciya a cikin rayuwar duniya da kuma lahira} [Ibrahim: 27].
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
التصنيف الشرعيتفسير الآيات، الحياة البرزخيةموضوعات الحديثالقرآن وعلومه، الإيمان باليوم الآخر