عربي - Arabic English Qafár af - Afar Afrikaans - Afrikanns Akan Shqip - Albanian አማርኛ - Amharic Հայերեն - Armenian অসমীয়া - Assamese Azərbaycanca - Azerbaijani Bamanankan - Bambara Bassa Bemba বাংলা - Bengali Bosanski - Bosnian Български - Bulgarian မြန်မာဘာသာ - Burmese Bisaya - Cebuano Cham Нохчий - Chechen chiCheŵa - Chewa 中文 - Chinese Адыгэбзэ - Circassian Hrvatski - Croatian Česky - Czech Dagbani Dansk - Danish فارسی دری - Dari Dendi ދިވެހި ބަސް - Dhivehi Nederlands - Dutch إستوني - Estonian Suomi - Finnish Français - French Fulfulde - Fula ქართული - Georgian Deutsch - German Ελληνικά - Greek ગુજરાતી - Gujrati Kreyòl ayisyen - Haitian Creole Hausa हिन्दी - Hindi Magyar - Hungarian Igbo Indonesia - Indonesian Italiano - Italian 日本語 - Japanese Jóola - Jola ಕನ್ನಡ - Kannada Қазақша - Kazakh ភាសាខ្មែរ - Khmer Kikuyu Ikinyarwanda - Kinyarwanda Ikirundi - Kirundi 한국어 - Korean كوردی سۆرانی - kurdish كوردي kurmancî - Kurmanji Kyrgyz ລາວ - Lao latviešu - Latvian Lingala lietuvių - Lithuanian Luganda Македонски - Macedonian Maguindanaon Malagasy - Malagasy Bahasa Melayu - Malay മലയാളം - Malayalam Mandinka मराठी - Marathi Mõõré - Moore नेपाली - Nepali أنكو - NKo Norwegian ଓଡ଼ିଆ - Odia oromoo - Oromo پښتو - Pashto فارسی - Persian Polski - Polish Portuguese ਪੰਜਾਬੀ - Punjabi Română - Romanian Русский - Russian Српски - Serbian Shona සිංහල - Sinhala Slovenščina - Slovenian Soomaaliga - Somali Soninke Sesotho - Sotho Español - Spanish Kiswahili - Swahili Svenska - Swedish Tagalog Тоҷикӣ - Tajik தமிழ் - Tamil తెలుగు - Telugu ไทย - Thai ትግረኛ - Tigrinya Türkçe - Turkish Ukrainian اردو - Urdu ئۇيغۇرچە - Uyghur Ўзбек - Uzbek Việt Nam - Vietnamese Wolof Yao Yorùbá - Yoruba Zarma زولو - Zulu
839 Hadisai
Kundin Hadisan Annabi
Rukunoni
Darajar hadisi
An ruwaito a
Mai ruwaya
Nuna duk masu ruwaya (11)
Wasu ribatattu sun zo wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ga wata mace daga cikin ribatattun nonanta yana zuba tana shayar da ɗanta, sai ga shi ta samu wani yaro a cikin ribatattun sai ta ɗauke shi, sai ta ɗanfara shi a cikinta ta shayar da shi, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce mana:
«Shin yanzu kuna zatan cewa wannan matar zata jefa ɗanta a cikin wuta?» muka ce: A'a, alhali ita tana da ikon ƙin jefa shi, sai ya ce:«Allah Ya fi tausayin bayinSa fiye da wannan matar ga ɗanta».
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - a abin da yake ruwatowa daga Allah - tsarki ya tabbatar masa Ya ɗaukaka - cewa Yace: "Ya bayina lallai ni Na haramta zalunci a kan kaina, kuma na sanyashi abin haramtawa, to, kada ku yi zalunci.
Ya ku bayina dukkaninku ɓatattu ne sai wanda Na shiryar da shi, ku nemi shiriyata in shiryar da ku.
Ya ku bayina, dukkaninku mayunwata ne sai wanda Na ciyar, ku nemi ciyarwata in ciyar da ku.
Ya ku bayina dukkaninku matsiraita ne sai wanda na tufatar da shi, ku nemi tufatarwata zan tufatar da ku.
Ya ku bayina lallai kuma yin laifi dare da rana, Ni kuma ina gafarta zunubai duka, ku nemi gafarata; Zan gafarta muku.
Ya ku bayania haƙiƙa ba za ku iya cutar da ni ba, ballantana ku cuceni, ba za ku iya amfanata ba, ballantana ku anfanar da Ni.
Ya ku bayina da a ce na farkonku da na ƙarshenku da muatnenku da aljanunku za su kasance a kan mafi taƙawar zuciyar mutum ɗaya daga cikinku hakan ba zai ƙara komai daga mulkina ba.
Ya ku bayina da a ce na farkonku da na ƙarshenku da mutanenku da aljanunku za su kasance a kan zuciyar mafi fajircin mutum ɗaya daga cikinku hakan ba zai rage wani abu daga mulkina ba.
Ya ku bayina da a ce na farkonku da na ƙarshenku da mutanenku da aljanunku za su tsaya a bigire ɗaya su tambayeni, sai in ba kowa tambayarsa hakan ba zai rage komai daga abin da ke wurina ba, sai dai abin da allura take tauyewa idan an shigar da ita kogi.
Ya ku bayina kaɗai ayyukankun ne ina kiyayesu gareku, sannan in cika muku su, to, wanda ya sami alheri, to, ya godewa Allah wanda ya samu wanin haka, to, kada ya zargi kowa sai kansa".
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi
«Lallai Allah Mai tsarki ne ba Ya karɓa sai mai tsarki, kuma Allah Ya umarci muminai da abinda Ya umarci Manzanni da shi, sai Maɗaukakin sarki Ya ce:
{Ya ku Manzanni ku ci daga tsarkaka kuma ku aikata aiki na gari, lallai cewa Ni Masani ne da abinda kuke aikatawa}.
Kuma Allah Maɗaukakin sarki Ya ce: {Ya ku waɗanda suka yi imani ku ci daga tsarkakan abinda muka azirta ku}. Sannan ya ambaci mutumin da yake tsawaita tafiya kansa ya cukurkuɗe, jikinsa ya yi ƙura, yana ɗaga hannayensa sama (yana cewa): Ya Ubangiji! ya Ubangiji! abin cinsa haramun ne, abin shansa haramun ne, abin ɗaurawarsa haramun ne, an shayar da shi da haram, to ta yaya za'a amsa masa ga hakan?».
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi
"Allah Zai damke kasa, Zai ninke sammai da hannunSa na dama, sannan Ya ce: Ni ne sarki, ina sarakunan kasa".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
"Ya ku mutane ! Lallai Allah Mai tsarki ne ba Ya karba sai mai tsarki, kuma Allah Ya umarci muminai da abinda Ya umarci Manzanni da shi, sai Ya ce:
{Ya ku Manzanni ku ci daga tsarkaka kuma ku aikata aiki na gari, lallai cewa Ni Masani ne da abinda kuke aikatawa}.
[al-Mu'uminun: 51] .
Kuma Ya ce: {Ya ku waɗanda suka yi imani ku ci daga tsarkakan abinda muka azirta ku}. [al:Baƙara: 172]. Sannan ya ambaci mutumin da yake tsawaita tafiya kansa ya cukurkuɗe, jikinsa ya yi ƙura, yana ɗaga hannayensa sama: Ya Ubangiji, ya Ubangiji, abin cinsa haramun ne, abin shansa haramun ne, abin ɗaurawarsa haramun ne, an shayar da shi da haram, to tayaya za'a amsa masa ga hakan?".
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi
«Lallai cewa Allah idan Ya so wani bawa sai Ya kira Jibril sai Ya ce: Lallai cewa Ni ina son wane to ka so shi, ya ce: Sai Jibril yaso shi, sannan ya yi kira a cikin sama sai ya ce: Lallai Allah Ya na son wane to kuso shi, sai waɗanda ke sama su so shi, sannan a sanya masa karɓuwa a cikin ƙasa.
Idan kuma Ya ƙi wani bawa sai Ya kira Jibril sai Ya ce; Lallai Ni ina ƙin wane to ka ƙi shi, ya ce sai (Mala’ika) Jibril ya ƙi shi, sannan sai ya yi kira a cikin waɗanda ke cikin sama lallai cewa Allah Yana ƙin wane to ku ƙishi, ya ce: Sai su ƙishi, sannan a sanya masa baƙin jini a cikin ƙasa».
Ingantacce ne Sahih Muslim
Lalle Allah Yana jinkirtawa azzalumi, har idan ya kama shi ba zai taɓa kufcewa ba)). Ya ce: Sannan ya Karanta: Kuma haka kamun Ubangijinka Yake idan ya damƙi alkaryu suna azzalumai, lalle damƙarSa mai raɗaɗi ce mai tsanani ce.
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Allah - Madaukakin sarki ya ce: ‘Dan Adam ya karyata Ni kuma hakan bai cancanci ya faru daga gare shi ba, ya aibanta Ni kuma hakan bai kamata ya faru daga gare shi ba.
Amma karyatawar shi gare Ni shi ne fadinsa: (Allah) ba zai dawo dani ba (bayan mutuwa) kamar yadda Ya halicce ni a farko, ba wai halittar ta farkon ita ce mafi sauki gareNi daga dawowa da shi ba, amma aibantaNi shi ne fadinsa a kaina: Allah Yana da Da, alhali Ni Daya ne kwal wanda ake nufinSa da bukata Ban haifa ba, ba’a kuma haifeNi ba, kuma babu daya da ya kasance tamka a gare Ni".
Ingantacce ne Bukhari ne ya rawaito shi.