Skip to content
839 Hadisai

Kundin Hadisan Annabi

Tace sakamako

14 daga cikin katuna 839

Cire tacewa
"Lallai Allah Yana kishi, muminima yana kishi, kishin Allah (shi ne) mumini ya zo wa abinda (Allah) ya haramta masa".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: ""Lallai Allah Ya ce: Wanda ya ya yi gaba da masoyiNa to na yi shelar yaki da shi, kuma bawaNa bai taba kusanta zuwa gare Ni ba da wani abu kamar abinda na farlanta masa ba, bawa Na ba zai gushe ba yana kusanta gareNi da nafilfili har sai Na soshi, idan Naso shi zan zama jinsa da yake ji da shi, da ganinsa da yake gani da shi, da hannunsa da yake dauka da shi, da kafarsa da yake tafiya da ita, kuma da zai rokeni sai na ba shi, kuma da zai nemi tsari da Ni sai Na tsare shi, kuma ban taba kai komo a kan yin wani abu kamar karbar ran mumini ba, yana kin mutuwa Ni kuma iNa ki masa wahalarsa"
Ingantacce ne Bukhari ne ya rawaito shi.
«Mafi soyuwar garuruwa a wurin Allah sune masallatansu, kuma mafi ƙin garuruwa a wurin Allah sune kasuwanninsu».
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi
"Ku kusanto ku daidaita, ku sani cewa babu wani daga cikinku da zai tsira da aikinsa". Suka ce: Ya Manzon Allah koda kaine?ya ce: "Koda nine sai dai idan Allah Ya lulluɓeni da rahamarSa da kuma falalarSa".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
"Allah ba Ya duba zuwa surorinku da dukiyoyinku, sai dai Yana duba zuwa zukatanku da ayyukanku".
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi
«Lallai Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: “Duk wanda ya yi gaba da masoyiNa to haƙiƙa na sanar da shi yaƙi, kuma bawa Na bai nemi kusanci gareni da wani abu mafi soyuwa gareNi ba daga abin da na wajabata masa, kuma bawaNa ba zai gushe ba yana neman kusanci daNi ba har sai na so shi, idan Na so shi sai in zama jinsa wanda yake ji da shi, da ganinsa wanda yake gani da shi, da hannunsa wanda yake damƙa da shi, da ƙafarsa wacce yake tafiya da ita, idan ya rokeNi lallai zan ba shi, idan ya nemi tsariNa lallai zan tsare shi ».
Ingantacce ne Bukhari ne ya rawaito shi.
«Lallai Allah Mai tsarki ne ba Ya karɓa sai mai tsarki, kuma Allah Ya umarci muminai da abinda Ya umarci Manzanni da shi, sai Maɗaukakin sarki Ya ce: {Ya ku Manzanni ku ci daga tsarkaka kuma ku aikata aiki na gari, lallai cewa Ni Masani ne da abinda kuke aikatawa}. Kuma Allah Maɗaukakin sarki Ya ce: {Ya ku waɗanda suka yi imani ku ci daga tsarkakan abinda muka azirta ku}. Sannan ya ambaci mutumin da yake tsawaita tafiya kansa ya cukurkuɗe, jikinsa ya yi ƙura, yana ɗaga hannayensa sama (yana cewa): Ya Ubangiji! ya Ubangiji! abin cinsa haramun ne, abin shansa haramun ne, abin ɗaurawarsa haramun ne, an shayar da shi da haram, to ta yaya za'a amsa masa ga hakan?».
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi
"Allah Zai damke kasa, Zai ninke sammai da hannunSa na dama, sannan Ya ce: Ni ne sarki, ina sarakunan kasa".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi