Skip to content
839 Hadisai

Kundin Hadisan Annabi

Tace sakamako

25 daga cikin katuna 839

Cire tacewa
«Lallai Allah Mai tsarki ne ba Ya karɓa sai mai tsarki, kuma Allah Ya umarci muminai da abinda Ya umarci Manzanni da shi, sai Maɗaukakin sarki Ya ce: {Ya ku Manzanni ku ci daga tsarkaka kuma ku aikata aiki na gari, lallai cewa Ni Masani ne da abinda kuke aikatawa}. Kuma Allah Maɗaukakin sarki Ya ce: {Ya ku waɗanda suka yi imani ku ci daga tsarkakan abinda muka azirta ku}. Sannan ya ambaci mutumin da yake tsawaita tafiya kansa ya cukurkuɗe, jikinsa ya yi ƙura, yana ɗaga hannayensa sama (yana cewa): Ya Ubangiji! ya Ubangiji! abin cinsa haramun ne, abin shansa haramun ne, abin ɗaurawarsa haramun ne, an shayar da shi da haram, to ta yaya za'a amsa masa ga hakan?».
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi
"Allah Zai damke kasa, Zai ninke sammai da hannunSa na dama, sannan Ya ce: Ni ne sarki, ina sarakunan kasa".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
"Ya ku mutane ! Lallai Allah Mai tsarki ne ba Ya karba sai mai tsarki, kuma Allah Ya umarci muminai da abinda Ya umarci Manzanni da shi, sai Ya ce: {Ya ku Manzanni ku ci daga tsarkaka kuma ku aikata aiki na gari, lallai cewa Ni Masani ne da abinda kuke aikatawa}. [al-Mu'uminun: 51] . Kuma Ya ce: {Ya ku waɗanda suka yi imani ku ci daga tsarkakan abinda muka azirta ku}. [al:Baƙara: 172]. Sannan ya ambaci mutumin da yake tsawaita tafiya kansa ya cukurkuɗe, jikinsa ya yi ƙura, yana ɗaga hannayensa sama: Ya Ubangiji, ya Ubangiji, abin cinsa haramun ne, abin shansa haramun ne, abin ɗaurawarsa haramun ne, an shayar da shi da haram, to tayaya za'a amsa masa ga hakan?".
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi
«‌Lallai cewa Allah idan Ya so wani bawa sai Ya kira Jibril sai Ya ce: Lallai cewa Ni ina son wane to ka so shi, ya ce: Sai Jibril yaso shi, sannan ya yi kira a cikin sama sai ya ce: Lallai Allah Ya na son wane to kuso shi, sai waɗanda ke sama su so shi, sannan a sanya masa karɓuwa a cikin ƙasa. Idan kuma Ya ƙi wani bawa sai Ya kira Jibril sai Ya ce; Lallai Ni ina ƙin wane to ka ƙi shi, ya ce sai (Mala’ika) Jibril ya ƙi shi, sannan sai ya yi kira a cikin waɗanda ke cikin sama lallai cewa Allah Yana ƙin wane to ku ƙishi, ya ce: Sai su ƙishi, sannan a sanya masa baƙin jini a cikin ƙasa».
Ingantacce ne Sahih Muslim
Lalle Allah Yana jinkirtawa azzalumi, har idan ya kama shi ba zai taɓa kufcewa ba)). Ya ce: Sannan ya Karanta: Kuma haka kamun Ubangijinka Yake idan ya damƙi alkaryu suna azzalumai, lalle damƙarSa mai raɗaɗi ce mai tsanani ce.
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Allah - Madaukakin sarki ya ce: ‘Dan Adam ya karyata Ni kuma hakan bai cancanci ya faru daga gare shi ba, ya aibanta Ni kuma hakan bai kamata ya faru daga gare shi ba. Amma karyatawar shi gare Ni shi ne fadinsa: (Allah) ba zai dawo dani ba (bayan mutuwa) kamar yadda Ya halicce ni a farko, ba wai halittar ta farkon ita ce mafi sauki gareNi daga dawowa da shi ba, amma aibantaNi shi ne fadinsa a kaina: Allah Yana da Da, alhali Ni Daya ne kwal wanda ake nufinSa da bukata Ban haifa ba, ba’a kuma haifeNi ba, kuma babu daya da ya kasance tamka a gare Ni".
Ingantacce ne Bukhari ne ya rawaito shi.
"Wani bawa ba zai suturta wani bawa a duniya ba sai Allah Ya suturta shi a ranar Alƙiyama".
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi
Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Allah - Mai girma da ɗaukaka - Yana cewa: Ni ina inda zatan bawaNa yake, kuma Ni ina tare da shi lokacin da yake ambatona, idan ya ambaceNi a cikin ransa zan ambace shi a cikin raiNa, idan ya ambaceni a cikin mutane zan ambace shi a cikin mutanen da suka fisu alheri, idan ya kusantoNi taki (ɗaya), Zan kusanto zuwa gare shi zira'i (ɗaya), idan ya kusanto zuwa gareNi zira'i (ɗaya), zan kusanto gare shi faɗin hannaye, idan ya zo miNi yana tafiya zan zo masa ina gaggawa".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi