Skip to content
839 Hadisai

Kundin Hadisan Annabi

Tace sakamako

25 daga cikin katuna 839

Cire tacewa
‘’Babu wani daga cikinku face sai Allah ya yi magana da shi, babu wani tafinta a tsakaninsu, sai ya duba zuwa daman sa ba zai ga komai ba face abinda ya aikata, sai ya yi duba zuwa hagunsa shima ba zai ga komai ba face abinda ya aikata, sai ya yi duba zuwa gabansa ba zai ga komai ba sai wuta wajen fuskarsa, to ku ji tsoron wuta ko da kuwa da gutsiren dabino ne".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
"Masu jin ƙai (Ubangiji) Al-Rahman yana jin ƙansu, ku ji ƙan mutanen ƙasa wanda ke sama zai ji ƙanku".
Ingantacce ne Abu Daud ne ya ruwaito shi da Kuma Tirmizi da Ahmad
Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce ga mai tabo mai tabon Abdulƙais: «‌Lallai kai kana da ɗabi'u biyu waɗanda Allah Yake sonsu: Haƙuri da kuma dangana».
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi
«Lallai Allah - Maɗaukakin sarki - Ya ce: “Duk wanda ya yi gaba da masoyiNa to haƙiƙa na sanar da shi yaƙi, kuma bawa Na bai nemi kusanci gareni da wani abu mafi soyuwa gareNi ba daga abin da na wajabata masa, kuma bawaNa ba zai gushe ba yana neman kusanci daNi ba har sai na so shi, idan Na so shi sai in zama jinsa wanda yake ji da shi, da ganinsa wanda yake gani da shi, da hannunsa wanda yake damƙa da shi, da ƙafarsa wacce yake tafiya da ita, idan ya rokeNi lallai zan ba shi, idan ya nemi tsariNa lallai zan tsare shi ».
Ingantacce ne Bukhari ne ya rawaito shi.
«Lallai Allah - Mai girma da ɗaukaka - ba Ya bacci, kuma ba ya kamata gareShi Ya yi bacci, Yana ƙasa da ma'auni kuma Yana ɗaga shi, ana ɗaga aikin dare kafin aikin rana zuwa gare Shi, da aikin rana kafin aikin dare, shamakinSa shi ne haske, da ace zai yaye shi da hasken fuskarSa ya ƙona inda ganinsa ya tiƙe daga halittarSa».
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi
Daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - a cikin abin da yake ruwaitowa daga Ubangijinsa - Mai girma da ɗaukaka - ya ce: Ya ce: "Lallai Allah Ya rubuta kyawawa (lada) da munana (alhaki), sannan Ya bayyana hakan, wanda ya yi nufin kyakkyawa bai aikatata ba, to, Allah zai rubuta masa kykkyawa cikakkiya, idan ya yi nufinsa sai ya aikatata, to, Allah Zai rubuta masa kyawawa goma a wurinsa zuwa ninki ɗari bakwai, zuwa ninki da yawa, wanda ya yi nufin mummuna bai aikatashi ba, to, Allah Zai rubuta kykkyawa cikakke, idan ya yi nufinsa sai ya aikatashi Allah Zai rubuta masa mummuna ɗaya".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Wasu ribatattu sun zo wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ga wata mace daga cikin ribatattun nonanta yana zuba tana shayar da ɗanta, sai ga shi ta samu wani yaro a cikin ribatattun sai ta ɗauke shi, sai ta ɗanfara shi a cikinta ta shayar da shi, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce mana: «‌Shin yanzu kuna zatan cewa wannan matar zata jefa ɗanta a cikin wuta?» muka ce: A'a, alhali ita tana da ikon ƙin jefa shi, sai ya ce:«‌Allah Ya fi tausayin bayinSa fiye da wannan matar ga ɗanta».
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - a abin da yake ruwatowa daga Allah - tsarki ya tabbatar masa Ya ɗaukaka - cewa Yace: "Ya bayina lallai ni Na haramta zalunci a kan kaina, kuma na sanyashi abin haramtawa, to, kada ku yi zalunci. Ya ku bayina dukkaninku ɓatattu ne sai wanda Na shiryar da shi, ku nemi shiriyata in shiryar da ku. Ya ku bayina, dukkaninku mayunwata ne sai wanda Na ciyar, ku nemi ciyarwata in ciyar da ku. Ya ku bayina dukkaninku matsiraita ne sai wanda na tufatar da shi, ku nemi tufatarwata zan tufatar da ku. Ya ku bayina lallai kuma yin laifi dare da rana, Ni kuma ina gafarta zunubai duka, ku nemi gafarata; Zan gafarta muku. Ya ku bayania haƙiƙa ba za ku iya cutar da ni ba, ballantana ku cuceni, ba za ku iya amfanata ba, ballantana ku anfanar da Ni. Ya ku bayina da a ce na farkonku da na ƙarshenku da muatnenku da aljanunku za su kasance a kan mafi taƙawar zuciyar mutum ɗaya daga cikinku hakan ba zai ƙara komai daga mulkina ba. Ya ku bayina da a ce na farkonku da na ƙarshenku da mutanenku da aljanunku za su kasance a kan zuciyar mafi fajircin mutum ɗaya daga cikinku hakan ba zai rage wani abu daga mulkina ba. Ya ku bayina da a ce na farkonku da na ƙarshenku da mutanenku da aljanunku za su tsaya a bigire ɗaya su tambayeni, sai in ba kowa tambayarsa hakan ba zai rage komai daga abin da ke wurina ba, sai dai abin da allura take tauyewa idan an shigar da ita kogi. Ya ku bayina kaɗai ayyukankun ne ina kiyayesu gareku, sannan in cika muku su, to, wanda ya sami alheri, to, ya godewa Allah wanda ya samu wanin haka, to, kada ya zargi kowa sai kansa".
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi