Skip to content
839 Hadisai

Kundin Hadisan Annabi

Tace sakamako

21 daga cikin katuna 839

Cire tacewa
«‌Lallai cewa Allah idan Ya so wani bawa sai Ya kira Jibril sai Ya ce: Lallai cewa Ni ina son wane to ka so shi, ya ce: Sai Jibril yaso shi, sannan ya yi kira a cikin sama sai ya ce: Lallai Allah Ya na son wane to kuso shi, sai waɗanda ke sama su so shi, sannan a sanya masa karɓuwa a cikin ƙasa. Idan kuma Ya ƙi wani bawa sai Ya kira Jibril sai Ya ce; Lallai Ni ina ƙin wane to ka ƙi shi, ya ce sai (Mala’ika) Jibril ya ƙi shi, sannan sai ya yi kira a cikin waɗanda ke cikin sama lallai cewa Allah Yana ƙin wane to ku ƙishi, ya ce: Sai su ƙishi, sannan a sanya masa baƙin jini a cikin ƙasa».
Ingantacce ne Sahih Muslim
Lalle Allah Yana jinkirtawa azzalumi, har idan ya kama shi ba zai taɓa kufcewa ba)). Ya ce: Sannan ya Karanta: Kuma haka kamun Ubangijinka Yake idan ya damƙi alkaryu suna azzalumai, lalle damƙarSa mai raɗaɗi ce mai tsanani ce.
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
"Wani bawa ba zai suturta wani bawa a duniya ba sai Allah Ya suturta shi a ranar Alƙiyama".
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi
Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Allah - Mai girma da ɗaukaka - Yana cewa: Ni ina inda zatan bawaNa yake, kuma Ni ina tare da shi lokacin da yake ambatona, idan ya ambaceNi a cikin ransa zan ambace shi a cikin raiNa, idan ya ambaceni a cikin mutane zan ambace shi a cikin mutanen da suka fisu alheri, idan ya kusantoNi taki (ɗaya), Zan kusanto zuwa gare shi zira'i (ɗaya), idan ya kusanto zuwa gareNi zira'i (ɗaya), zan kusanto gare shi faɗin hannaye, idan ya zo miNi yana tafiya zan zo masa ina gaggawa".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Ubangijimmu maɗaukaki Yana sauka a kowanne dare, zuwa sama makusanciya, lokacin da ɗaya bisa uku na dare ya saura yana cewa: Wa zai roƙeni in amsa masa,?? wa zai tambaye ni in ba shi, ?? wa zai nemi gafarata in gafarta masa ??
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi