Skip to content
839 Hadisai

Kundin Hadisan Annabi

Tace sakamako

5 daga cikin katuna 839

Cire tacewa
"Ya Allah kada Ka maida kabarina gunki, Allah Ya la'anci mutanen da suka maida kaburburan Annabawansu masallatai".
Ingantacce ne Ahmad ne ya rawaito shi
«Mafi soyuwar garuruwa a wurin Allah sune masallatansu, kuma mafi ƙin garuruwa a wurin Allah sune kasuwanninsu».
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi
«Kada ku hana bayin Allah mata (zuwa) masallatan Allah, saidai su fita alhali ba su yi mummunar shiga ba».
Hasan ne Abu Dawud ne Ya Rawaito shi
«Idan ɗayanku ya shiga masallaci to ya yi wa Annabi salati kuma ya ce: Ya Allah Ka buɗe mini ƙofofin rahamarKa, idan kuma zai fita to ya yi wa Annabi sallama sannan ya ce: Ya Allah Ka tsareni daga Shaiɗan abin jefewa». (Riwayar) Hakim: «Idan zai fita to ya yi wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sallama, sannan ya ce: Ya Allah Ka tsareni daga Shaiɗan abin jefewa».
Hasan ne Ibnu Majah da Hakim ne suka Rawaito shi
«(Mutum) bakwai Allah - Maɗaukakin sarki - Zai inuwantar da su a cikin inuwarSa ranar da babu wata inuwa sai inuwarSa: Shugaba adali, da saurayin da ya taso a cikin bautar Allah, da mutumin da zuciyarsa ta rataya da masallatai, da mutum biyu da suka so juna saboda Allah, sun haɗu saboda Shi kuma suka rabu saboda Shi, da mutumin da mace mai matsayi da kyau ta neme shi sai ya ce: Lallai ni ina jin tsoron Allah, da mutumin da ya yi sadaka sai ya ɓoyeta har (hannunsa) na hagu bai san abinda (hannunsa) na dama ya ciyar ba, da mutumin da ya ambaci Allah shi kaɗai sai idanuwansa suka zubar da hawaye».
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi