Skip to content
839 Hadisai

Kundin Hadisan Annabi

Tace sakamako

12 daga cikin katuna 839

Cire tacewa
Cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan zai yi sallar Asuba sai ya zauna a wurin sallarsa har sai rana ta ɓullo tana ɗage, kuma ya ce: Ya kasance ba ya tashi daga wurin da ya yi sallar Asuba har sai rana ta ɓullo, idan rana ta ɓullo sai ya tashi, kuma sun kasance suna tattaunawa sai su shiga labari cikin al'amarin Jahiliyya, sai su yi dariya shi kuma ya yi murmushi.
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi
Cewa Ummu Salama ta gayawa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cewa ta ga wata coci a kasar Habasha, ana kiranta Mariya, sai ta fadi duk abubuwan da ta gani a can na Hotuna, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wadannan wasu mutane ne idan bawa na gari ya mutu daga cikinsu, ko kuma mutumin kirki, sai su gina masallaci akan kabarinsa, kuma su yi masa wadannan hotunan, wadannan su ne ashararen mutane a wajen Allah".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
"Sallah a cikin masallacina wannan (ita ce) mafi alheri daga sallah dubu a cikin waninsa sai dai Masallaci mai alfarma".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
«(Mutum) bakwai Allah - Maɗaukakin sarki - Zai inuwantar da su a cikin inuwarSa ranar da babu wata inuwa sai inuwarSa: Shugaba adali, da saurayin da ya taso a cikin bautar Allah, da mutumin da zuciyarsa ta rataya da masallatai, da mutum biyu da suka so juna saboda Allah, sun haɗu saboda Shi kuma suka rabu saboda Shi, da mutumin da mace mai matsayi da kyau ta neme shi sai ya ce: Lallai ni ina jin tsoron Allah, da mutumin da ya yi sadaka sai ya ɓoyeta har (hannunsa) na hagu bai san abinda (hannunsa) na dama ya ciyar ba, da mutumin da ya ambaci Allah shi kaɗai sai idanuwansa suka zubar da hawaye».
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi