Skip to content
839 Hadisai

Kundin Hadisan Annabi

Tace sakamako

10 daga cikin katuna 839

Cire tacewa
"ku daidaita sahunku, don daidaita shahu na daga cikar sallah".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
«Mafi soyuwar garuruwa a wurin Allah sune masallatansu, kuma mafi ƙin garuruwa a wurin Allah sune kasuwanninsu».
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi
Wata rana muna cikin masallaci tare da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ga wani balaraben ƙauye ya zo, sai ya miƙe yana fitsari a cikin masallaci, sai sahabban Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - suka ce: Tsaya tsaya, sai ya ce: Sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «‌Kada ku yanke masa fitsarinsa, ku ƙyake shi» sai suka rabu da shi har saida ya gama fitsari, sannan Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kira shi sai ya ce masa: «‌Lallai waɗannan masallatan badan fitsari aka yi su ba, ko dan ƙazanta , kawai su dan ambatan Allah ne - Mai girma da ɗaukaka, da sallah da kuma karatun alƙur'ani» ko kamar yadda Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Sai ya umarci wani mutum daga cikin mutanen sai ya zo da guga na ruwa sai ya zuba a kansa.
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
"Idan ɗayanku zai shiga masallaci, to, ya ce: Ya Allah Ka buɗe min ƙofofin rahamarKa, idan zai fita, to, ya ce: Ya Allah ina roƙonKa daga falalarKa".
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi
Cewa Usman ɗan Affan ya yi nufin gina masallaci sai mutane suka ƙi hakan, suka so ya bar shi a kan yadda yake, sai ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: "Wanda ya gina masallaci saboda Allah; Allah Zai gina masa kwatankwacinsa a cikin aljanna".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
"Idan ɗayanku ya shiga masallaci, to, ya yi sallah raka'a biyu kafin ya zauna".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan zai yi sallar Asuba sai ya zauna a wurin sallarsa har sai rana ta ɓullo tana ɗage, kuma ya ce: Ya kasance ba ya tashi daga wurin da ya yi sallar Asuba har sai rana ta ɓullo, idan rana ta ɓullo sai ya tashi, kuma sun kasance suna tattaunawa sai su shiga labari cikin al'amarin Jahiliyya, sai su yi dariya shi kuma ya yi murmushi.
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi
Cewa Ummu Salama ta gayawa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cewa ta ga wata coci a kasar Habasha, ana kiranta Mariya, sai ta fadi duk abubuwan da ta gani a can na Hotuna, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wadannan wasu mutane ne idan bawa na gari ya mutu daga cikinsu, ko kuma mutumin kirki, sai su gina masallaci akan kabarinsa, kuma su yi masa wadannan hotunan, wadannan su ne ashararen mutane a wajen Allah".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi