Skip to content
839 Hadisai

Kundin Hadisan Annabi

Tace sakamako

52 daga cikin katuna 839

Cire tacewa
"Tafkina tafiyar wata ne, ruwansa ya fi nono fari, kamshinsa ya fi almiski kanshi, kofunansa kamar taurarin sama ne, wanda ya sha daga gare shi ba zai yi kishirwa ba har abada".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
"Lallai wannan al'amarin zai kai inda dare da rana suka kai, kuma Allah ba Zai bar wani gidan bulo ko na gashi ba sai Allah Ya shigar da wannan addinin cikinsa, da girman mai girma ko da ƙasƙancin kaskantacce, buwaya ce da Allah Yake ɗaukaka musulunci da ita, da ƙasƙancin da Allah Yake ƙasƙantar da kafirci da shi" Tamimi al-Dari ya kasance yana cewa: Haƙiƙa na san hakan a iyalan gidana, haƙiƙa wanda ya musulunta a cikinsu alheri da ɗaukaka da buwaya ya same shi, wanda yake kafiri a cikinsu kuma ƙasƙanci da wulaƙanci da jiziya sun same shi .
Ingantacce ne Ahmad ne ya rawaito shi
«Idan aka ajiye jana'iza (gawa) maza suka ɗauketa akan kafadinsu idan ta kasance ta gari ce zata ce: Ku kaini, idan ba ta gari ba ce kuwa zata ce: Ya kaicanta ina zasu tafi da ita? kowane abu yana jin sautinta sai mutum kawai, da ace ya ji shi (sautin) da ya suma».
Ingantacce ne Bukhari ne ya rawaito shi.
"Wanda ya shaida cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Shi kadai baShi da abokin tarayya, kuma Annabi Muhammadu bawanSa ne kuma ManzonSa ne, kuma Annabi Isa bawan Allah ne kuma ManzonSa ne kalmarSa ne da ya jefa ta ga nana Maryamu kuma Ruhi ne daga gare Shi, kuma aljanna gaskiya ce haka wuta ma gaskiya ce, Allah Zai shigar da shi Aljanna akan aikin da yake akansa".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi