عربي - Arabic English Qafár af - Afar Afrikaans - Afrikanns Akan Shqip - Albanian አማርኛ - Amharic Հայերեն - Armenian অসমীয়া - Assamese Azərbaycanca - Azerbaijani Bamanankan - Bambara Bassa Bemba বাংলা - Bengali Bosanski - Bosnian Български - Bulgarian မြန်မာဘာသာ - Burmese Bisaya - Cebuano Cham Нохчий - Chechen chiCheŵa - Chewa 中文 - Chinese Адыгэбзэ - Circassian Hrvatski - Croatian Česky - Czech Dagbani Dansk - Danish فارسی دری - Dari Dendi ދިވެހި ބަސް - Dhivehi Nederlands - Dutch إستوني - Estonian Suomi - Finnish Français - French Fulfulde - Fula ქართული - Georgian Deutsch - German Ελληνικά - Greek ગુજરાતી - Gujrati Kreyòl ayisyen - Haitian Creole Hausa हिन्दी - Hindi Magyar - Hungarian Igbo Indonesia - Indonesian Italiano - Italian 日本語 - Japanese Jóola - Jola ಕನ್ನಡ - Kannada Қазақша - Kazakh ភាសាខ្មែរ - Khmer Kikuyu Ikinyarwanda - Kinyarwanda Ikirundi - Kirundi 한국어 - Korean كوردی سۆرانی - kurdish كوردي kurmancî - Kurmanji Kyrgyz ລາວ - Lao latviešu - Latvian Lingala lietuvių - Lithuanian Luganda Македонски - Macedonian Maguindanaon Malagasy - Malagasy Bahasa Melayu - Malay മലയാളം - Malayalam Mandinka मराठी - Marathi Mõõré - Moore नेपाली - Nepali أنكو - NKo Norwegian ଓଡ଼ିଆ - Odia oromoo - Oromo پښتو - Pashto فارسی - Persian Polski - Polish Portuguese ਪੰਜਾਬੀ - Punjabi Română - Romanian Русский - Russian Српски - Serbian Shona සිංහල - Sinhala Slovenščina - Slovenian Soomaaliga - Somali Soninke Sesotho - Sotho Español - Spanish Kiswahili - Swahili Svenska - Swedish Tagalog Тоҷикӣ - Tajik தமிழ் - Tamil తెలుగు - Telugu ไทย - Thai ትግረኛ - Tigrinya Türkçe - Turkish Ukrainian اردو - Urdu ئۇيغۇرچە - Uyghur Ўзбек - Uzbek Việt Nam - Vietnamese Wolof Yao Yorùbá - Yoruba Zarma زولو - Zulu
839 Hadisai
Kundin Hadisan Annabi
Rukunoni
Darajar hadisi
An ruwaito a
Mai ruwaya
Nuna duk masu ruwaya (30)
"Lallai Allah ba ya zalintar mumini wani kyakkyawa, za'a ba shi a duniya kuma za’a yi masa sakayya da ita a lahira.
Amma kafiri sai a ciyar da shi da kyakkyawan abinda ya aikata saboda Allah a duniya, har idan ya tafi lahira, (zai zama) ba shi da wani kyakkyawa da za’a yi masa sakayya da shi".
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi
Cewa wani mutum ya tambayi Annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - daga alkiyama, sai ya ce: Yaushe ne alkiyama? Ya ce: "Mai ka tanadar mata?" Ya ce: Babu komai, sai dai ni ina son Allah da ManzonSa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ya ce; "Kai kana tare da wanda ka so" Anas ya ce: Bamu taba farin ciki da wani abu ba, irin farin cikinmu da faɗin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: "Kai kana tare da wanda ka so" Anas ya ce: Ni ina son Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da Abubakar, da Umar, kuma ina kaunar in kasance tare da su dan son da nake musu, koda ban yi aiki irin aikinsu ba.
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
"Lallai daga cikin alamomin tashin Alkiyama, za’a dauke ilimi, jahilci zai yi yawa, zina zata yawaita, za’a yawaita shan giya, maza za su yi karanci, mata za su yi yawa, har sai ya kasance mata hamsin mutum daya ne yake kula da su".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi