Skip to content
839 Hadisai

Kundin Hadisan Annabi

Tace sakamako

3 daga cikin katuna 839

Cire tacewa
Na kasance ina rubuta dukkan abin da na ji shi daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ina son haddace shi, sai Ƙuraishawa suka hana ni, suka ce: Shin ka dinga rubuta dukkan abin da ka ji shi daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, alhali Manzon Allah -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - mutum ne yana magana a cikin fushi da yarda? sai na dakata daga rubutun, sai na fadawa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, hakan sai ya yi nuni da 'yan yatsunsa zuwa bakinsa, sai ya ce: "Ka rubuta, na rantse da wanda raina yake a hannunSa babu abin da zai fito daga cikinsa sai gaskiya".
Ingantacce ne Abu Dawud ne Ya Rawaito shi
Na tafi a cikin jama'ar Banu Amir zuwa ga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, Sai muka ce: Kai ne shugabanmu, sai ya ce: "Shugaba Shi ne Allah", muka ce: Mafificinmu a fifiko, kuma mafi girmanmu a kyauta, sai ya ce: "Ku fadi maganarku, ko wani bangare na maganarku, kada Shaidan ya yi amfani daku".
Ingantacce ne Abu Dawud ne ya Rawaito shi da Kuma Ahmad
"Ku saurara, kada wani mutum Hadisi ya je masa daga gareni alhali shi yana kishingide akan mazauninsa sai ya ce: Tsakanin mu da ku littafin Allah, abinda muka samu na halal a cikinsa mu halattashi, abinda muka samu a cikinsa na haram mu haramtashi, kuma lallai abinda Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya haramta to kamar abinda Allah Ya haramtane".
Ingantacce ne Abu Dawud da Tirmizi da Ibn Majah ne Suka Rawaito shi